Da Dumi-Dumi: Zanga-Zanga ta ɓarke a Sokoto, Mutane sun bukaci a sako waɗan da suka kashe Debora

Da Dumi-Dumi: Zanga-Zanga ta ɓarke a Sokoto, Mutane sun bukaci a sako waɗan da suka kashe Debora

  • Matasa sun fito zanga-zanga sun manaye tituna a wasu sassan jihar Sokoto kan kama wasu mutum 2 da zargin kashe ɗalibar da ta zagi Annabi
  • Masu zanga-zangar sun bukaci hukumomi su sako mutanen da suka tsare biyo bayan rikicin da ya faru a Kwalejin Shehu Shagari
  • Lamarin ya fara ne bayan wata ɗaliba yar aji biyu ta yi kalamai marasa daɗi da zagin Manzon Allah (SAW)

Sokoto - Mutane sun ɓarke da zanga-zanga kan tituna a wasu sassan jihar Sokoto ranar Asabar kan kama wasu da ake zargin su da kashe ɗalibar da ta yi batanci ga Annabi (SAW).

Daily Trust ta rahoto cewa wata ɗaliba yar aji biyu a makarantar horar da malamai ta Shehu Shagari, Debora Samuel, ta rasa rayuwarta hannun jama'a bisa zargin ta zagi Annabi Muhammad (SAW).

Kara karanta wannan

Dalibai mata na jami'o'i biyu a Arewa zasu fito tituna zanga-zanga tsirara kan yajin aikin ASUU

Matasa sun fito zanga-zanga a Sokoto.
Da Dumi-Dumi: Zanga-Zanga ta ɓarke a Sokoto, Mutane sun bukaci a sako waɗan da suka kashe Debora Hoto: Hafizu Ali/facebook
Asali: Facebook

Mutanen da suka fito zanga-zangar sun ɗaga Alluna da aka yi rubutu daban-daban kamar, "ku sako yan uwan mu Musulmai," "Musulmai ba yan ta'adda bane," da sauran su.

Tun kafin fara zanga-zangan, Jami'an tsaro suka mamaye wurare masu muhimmanci wanda ya haɗa da fadar mai martaba Sarkin Musulmi dake cikin garin Sokoto.

Wani mai amfani da kafar sada zumunta, Jefiter John, ya yi kira ga mazauna Sokoto su zauna a gida kuma su guji zuwa inda ake zanga-zangan.

Asalin abinda ya faru a Sokoto

Bayanai sun nuna cewa lamarin ya soma ne tun daga dandalin WhatsApp, inda mamaciyar da yi batanci da zage-zage ga fiyayyen halitta Annabi Muhammad (SAW).

Ɗaya daga cikin mutanen da ke dandalin wanda aka buɗe dan yan ajin su, ya tura wani abu da ya shafi Addini. Yayin da take martani, Debora, ta yi kalamai ma su muni ga Annabi, Premium times ta rahoto.

Kara karanta wannan

Batanci Ga Annabin Rahma (SAW), Dr Sani Umar Rijiyar Lemo

A wani labarin kuma Dirama a Kano yayin da tawagar Kwankwaso ta dira gidan Shekarau awanni bayan tafiyar Ganduje

Siyasar Kano ta ƙara rikicewa musamman tsakanin gwamna Abdullahi Umar Ganduje da Sanata Ibrahim Shekarau.

Bayan ziyarar Ganduje gidan Shekarau don hana shi komawa NNPP, Kwankwaso ya tura tawaga kafin zuwansa gidan Shekarau.

Asali: Legit.ng

Online view pixel