Wata Mata Ta Jefi Ma'aikatan Lantarki Da Duwatsu, Ta Kuma Lalata Musu Lada Yayin Da Suka Zo Yanke Mata Wuta

Wata Mata Ta Jefi Ma'aikatan Lantarki Da Duwatsu, Ta Kuma Lalata Musu Lada Yayin Da Suka Zo Yanke Mata Wuta

  • Wata Minotu Shodimu, mai shekaru 39 ta gurfana gaban kotun majistaren Ebute Meta da ke Legas bisa zarginta da lalata tsanin kamfanin raba wutar lantarkin Eko (EKEDC)
  • Matar wacce tireda ce a Ebute Meta ta na fuskantar tuhuma bisa laifuka biyu, na farko lalata kayan aikin kamfani sai kuma tayar da zaune tsaye
  • Kamar yadda mai gabatar da kara ya bayyana, ta lalata tsanin kamfanin mai kimar N120,000 ne bayan ma’aikata sun je yankar wuta a anguwarsu akan rashin biyan kudi

Legas - An gurfanar da Minotu Shodimu, mai shekaru 39 gaban kotun majistaren Ebute Meta da ke Jihar Legas bisa zarginta da lalata tsanin Kamfanin Rarraba Wutar Lantarkin Eko (EKEDC).

Jaridar Vanguard ta ce wacce ake karar, tireda ce da ke zama a gida mai lamba 58 a titin Abule-Nla kusa da titin Apapa a Ebute Meta, kuma an gurfanar da ita ne bisa zarginta da aikata laifuka biyu.

Kara karanta wannan

'Batanci: Jakadiyar Birtaniya Ta Ce Dole a Hukunta Waɗanda Suka Kashe Ɗalibar Sokoto

Wata mata ta jefi ma'aikatan lantarki da duwatsu, ta kuma lalata musu lada
Ana zargin wata mata da lalata tsanin kamfanin rarraba wutar lantarki da kuma jifan ma’aikatan kamfanin. Hoto: The Punch.
Asali: Twitter

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Na farko shi ne ta lalata kayan aiki sannan kuma ta tayar da zaune tsaye a anguwar. Sai dai ba ta amsa duk laifukan ba.

Ta yi amfani da karfi wurin lalata tsanin mai kimar N120,000

Mai gabatar da kara, kamar The Punch ta nuna, ASP Jimah Iseghede, ya sanar da kotu cewa ta aikata laifin ne a ranar 26 ga watan Fabrairu da misalin karfe 10:30 na safe a gida mai lamba ta 58 a titin Abule-Nla kusa da titin Apapa a Ebute Meta.

A cewarsa ta yi amfani da karfi wurin janye tsanin mai kimar N120,000 wanda na kamfanin EKEDC ne, inda ta lalata shi gaba daya.

Lamarin ya faru ne yayin da ma’aikacin EKEDC ya je harabar gidan matar yayin da ya yi yunkurin yanke wuta saboda bashin kudin da kamfanin ke binsu.

Kara karanta wannan

Sokoto: An kama wadanda suka kashe dalibar da ake zargin ta zagi Annabi

Alkali ta bayar da belin matar a N50,000

Iseghede ya zargi wacce ake karar da hada kai da wasu wurin tayar da tarzoma tare da kai wa ma’aikatan kamfanin farmaki har da jifarsu.

Laifin da ake zarginsu da aikatawa ya ci karo da Sashi na 168(D) da 350 na dokar masu laifuka ta Jihar Legas, 2015.

Alkalin kotun, Mrs T.O Abayomi, ta bayar da belin matar a N50,000 tare da bukatar ta gabatar da tsayayyu biyu.

Sannan alkalin ta dage sauraron karar zuwa ranar 13 ga watan Yuni don ci gaba da shari’ar.

Jigawa: 'Yan Hisbah sun kama mutum 47 suna sheƙe ayansu, ciki har da mata 16, an ƙwace kwallaban giya 745

A wani labarin, Hukumar Hisbah reshen jihar ta kama mutane 47 da ake zargin su na aikata rashin da’a ciki har da mata 16 kamar yadda

The Nation ta ruwaito. Kwamandan rundunar ta jihar, Malam Ibrahim Dahiru ne ya tabbatar da kamen ta wata hira da menama labarai su ka yi da shi jiya a Dutse, babban birnin jihar.

Kara karanta wannan

Babu abin da zai hana PDP karbe mulkin Najeriya a 2023, In ji Ayu

Bisa ruwayar jaridar The Nation, Dahiru ya ce a cikin wadanda aka kama har da wadanda ake zargin karuwai ne su 16.

Kuma an kama su ne bayan kai samamen da hukumar ta yi a gidajen giya, gidajen karuwai da sauran wuraren da mutanen banza ke zama.

Asali: Legit.ng

Online view pixel