Yajin aikin ASUU: Daliban Najeriya sun gano mafita, za su tara wa lakcarori kudi kawai

Yajin aikin ASUU: Daliban Najeriya sun gano mafita, za su tara wa lakcarori kudi kawai

  • Kungiyar daliban Najeriya ta bayyana cewa za a fara tara wa ASUU kudade domin malamai su koma makaranta kowa ya huta
  • Kodinetan NANS na shiyyar Kudu maso Yamma Kwamred Tegbe Stephen ne ya bayyana hakan a wata tattaunawa ta musamman da Legit.ng ta yi da shi
  • A halin da ake ciki, kungiyar kwadago ta Najeriya, a jiya ta sha alwashin shiga yajin aikin da ASUU ke ci gaba da yi, idan har FG ta gaza shawo kan matsalolin da kungiyar ta gabata

Najeriya - Kungiyar daliban Najeriya ta kasa ta bayyana shirinta na tara kudade ga kungiyar malaman jami’o’i (ASUU), domin mayar da malaman ajujuwa, inda ta bayyana cewa halin ko in kula na gwamnatin Najeriya ne ya sa su bin ta wannan hanyar.

Kara karanta wannan

Rokon da Shugaba Buhari ya yi, ya fada a kan kunnen kashi, ASUU ta cigaba da yajin-aiki

Kodinetan NANS na shiyyar Kudu Maso Yamma, Kwamared Tegbe Stephen, a wata tattaunawa ta musamman da Legit.ng, ya koka da yadda ake ci gaba da yajin ASUU, inda ya bayyana damuwa ga sake shelanta yajin aikin makwanni 12 da ASUU ta yi a makon nan.

Yadda dalibai ke nemawa ASUU mafita
Yajin aikin ASUU: Daliban Najeriya sun gano mafita, za su tara wa lakcarori kudade | Hoto: thenationonlineng.net
Asali: UGC

Ku tuna cewa duk wata tattaunawar da aka yi tsakanin gwamnati da kungiyar malaman ta ASUU ta kare ne ba tare da fitar da matsaya mai dorewa ba.

Hakan ya sa aka sake bude wani batun tattaunawa daga gwamnatin Najeriya, inda ta yi alkawarin fara aikin warware matsalolin a wannan makon.

Sai dai a yayin da ake kokarin dawowa tattaunawar, kungiyar ASUU ta sanar da tsawaita yajin aikin na tsawon makonni 12.

Matsayar Kwamared Tegbe

Sai dai Kwamared Tegbe ya shaida mana cewa, bayan shiru da gwamnati da masu mulki suka yi, ya kamata su shirya fuskantar fushin daliban Najeriya a Kudu maso Yamma. Ya ce a shirye suke su aiwatar da umarnin kungiyar dalibai ta kasa.

Kara karanta wannan

'Karin Bayani: Buhari Ya Roƙi ASUU Ta Janye Yajin Aiki, Ya Ba Wa Ɗalibai Haƙuri

Hukumar NANS ta kasa ta umurci dukkan shiyyoyin ta da ke fadin kasar nan da su rufe hanyoyin gwamnatin tarayya na tsawon awanni 3 a rana domin nuna rashin amincewarsu da tsawaita yajin aikin ASUU.

A cewar Tegbe:

“Za mu yi taro a Kudu maso Yamma don samo kudade saboda warware matsalolin ASUU tunda gwamnati ta nuna wa duniya cewa ba ta da wani abin da za ta iya yi.
“Matakin kungiyar ba wai kawai ilimi ya gurgunta ba, har ma da sassa daban-daban na tattalin arziki kuma babu shakka sun yi illa ga tattalin arzikin Najeriya ko muna so ko ba mu so.
“Ba za mu iya misalta matsalar da ke tattare da sakamakon ci gaban yajin aikin ASUU ba. Dalibanmu suna shan fama da mummunar illa, tun daga gundura daga sassan karatunsu daban-daban har zuwa ga tsanar karatun gaba daya.
"Duk irin wadannan za su iya kaiwa ga rashin samar da sakamako mai kyau na ilimi, ba a magana kuma game da tsawaitar lokaci da wasu da dama da suke fama da su a sakamakon wannan."

Kara karanta wannan

Yajin aikin ASUU: Daliban jami'a sun fusata, sun ba lakcarori da gwamnati wa'adi su bude jami'o'i

Da yake karin haske, kodinetan ya ce:

“A madadin NANS Kudu maso Yamma da kuma ko’odinetan kungiyar, muna Allah wadai da wannan lamari da kuma rawar da gwamnatin tarayya ke takawa a rayuwar daliban Najeriya a halin yanzu."

Wakilin Legit.ng Hausa a jihar Gombe ya gana da daya daga cikin shugabannin NANS a Arewacin Najeriya da ke karatun digiri na biyu a jami'ar tarayya da ke Kashere a Gombe, wanda ya nemi a sakaya sunansa saboda tsoron abin da ka iya biyo bayan kalamansa ya ce:

"Batun tara kudi ga malaman jami'a ma bai taso ba. Ta yaya daliban Najeriya za su iya hada kudaden da malaman ke nema?
"Bayan haka, idan aka warware matsalar a yanzu amma ba a daidaita tsakanin gwamnati da ASUU ba, bukatun dai na nan, na tabbata an yi ne ba a yi ba.
"Mafita shi ne, ASUU su yafe, domin suna da son zuciya su ma. Ba ta kananan malaman jami'a suke ba, suna yi ne don aljihunsu, ni shaida ne saboda a jami'a nake aiki.

Kara karanta wannan

Ku share ASUU ku koma aji: Shawarin gwamnan APC ga lakcarorin da ke yajin aiki

"Gwamnati kuma ta ji tsoron Allah ta saurari ASUU. ASUU 'yan kasa ne kuma ma'aikatan gwamnati, gwamnati uwa ce bai kamata ta yi shuru al'amari ya zama abu daban ba."

Yajin aikin ASUU: Daliban jami'a sun fusata, sun ba lakcarori da gwamnati wa'adi su bude jami'o'i

A wani labarin, kungiyar dalibai ta kasa (NANS) reshen kudu maso gabas ta baiwa gwamnatin tarayya da kungiyar malaman jami’o’i (ASUU) wa’adin kwanaki tara su bude dukkan jami’o’in gwamnati.

Ko’odinetan shiyyar NANS ta Kudu maso Gabas, Mista Moses Onyia, ya ba da wa’adin ne a cikin wata sanarwa da babban mai taimaka masa kan harkokin yada labarai, Lillian Orji, ya fitar a madadinsa, a ranar Talata a Enugu.

ASUU, a ranar Litinin, 9 ga watan Mayu, ta tsawaita yajin aikin gargadi na watanni uku da karin wasu watanni ukun, wanda ta shiga tun a ranar 14 ga Fabrairu, 2022, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Ta kanmu mu ke, ba ta kashe N100m ba: Fulani sun musanta sayen fom ga Jonathan

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.