Ana shirin fara jarrabawar WAEC, babu dalibi ko 1 da ya yi rajista a Sokoto da Zamfara

Ana shirin fara jarrabawar WAEC, babu dalibi ko 1 da ya yi rajista a Sokoto da Zamfara

  • WAEC ta bayyana irin shirye-shiryen da ta ke yi a game da jarrabawar WASCCE na shekarar bana
  • Hukumar ta koka da cewa makarantun gwamnati ba su gama kawo sunayen masu jarrabawa ba
  • Babu dalibin makarantar gwamnati ko daya da aka yi wa rajista a kaf jihohin Zamfara da Sokoto

Abuja - Makarantun gwamnatin da ake da su a jihohin Sokoto da Zamfara, ba su aikawa hukumar WAEC sunan wani dalibin da zai zana jarrabawa WASCCE ba.

Daily Trust ta ce shugaban hukumar WAEC na reshen Najeriya, Patrick Areghan ya bayyana haka a lokacin da ya zanta da manema labarai a ranar Litinin dinnan.

Areghan ya yi bayanin tanadin da hukumar tayi domin shiryawa jarrabawar shekarar bana, wanda za a fara daga 16 ga watan Mayu zuwa 23 ga watan Yuni.

Kara karanta wannan

Karin bayani: Tambuwal ya gana da malaman Islama kan batun dalibar da ta zagi Annabi

Yayin da makarantun kudi suka yi wa daliban da za su yi jarrabawar a shekarar nan rajista, Mista Areghan ya ce makarantun gwamnati ba su yi rajistar yaransu ba.

Jami’in hukumar jarrabawar ya ce ba su san abin da ya hana makarantun gwamnatin yin hakan ba.

Sai an yi hattara a 2022

Idan aka tafi a haka, ba za a samu wani dalibin makarantar gwamnati daga jihohin Zamfara da Sokoto da zai zana wannan jarrabawa ta gama karatun sakandare ba.

Jarrabawar WAEC
'Yan makaranta su na jarrabawa a Ghana Hoto: learninghana.com
Asali: UGC

Rahoton ya ce WAEC ta ja kunnen makarantun da suke yi wa dalibai rajista a makare, ta ce ba za ta yarda da wannan sakacin ba, domin hakan na jawo koma-baya.

Tribune ta ce sama da mutane miliyan 1.6 suka yi rajistar rubuta jarrabawar bana daga makarantu 20, 222. Daga ciki akwai maza 800, 055 da mata 800, 724.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Shugaban Hadaddiyar Daular Larabawa ya rigamu gidan gaskiya

Za a rubuta jarrabawar kammala sakandaren ne a fannoni 76 a zama 197. Manya malaman sakandare kusan 30, 000 ne za ayi amfani da su wajen aikin sa ido.

NIN da satar amsar jarrabawa

Har ila yau, Areghan ya ce duk da ana amfani da lambar NIN wajen rajista, amma ba dole sai da shi ba. An yi hakan ne saboda gudun a hana yara rubuta jarrabawar.

A game da sha’anin satar amsar jarrabawa ba, WAEC ta dauki matakai masu tsauri kamar yadda majalisar NEC mai lura da harkar jarrabawa a Najeriya tayi tanadi.

Za mu kashe JAMB da WAEC - Garba

Kwanaki mu ka rahoto 'dan takarar shugaban kasa a APC, Malam Adamu Garba II ya ce zai kawo tsare-tsaren da za su inganta harkar ilmi idan ya samu mulki.

Adamu Garba ya yi bayani cewa zai ba kowane yaro damar zuwa makarantun gaba da sakandare ta hanyar soke hukumomin WAEC, NECO, JAMB har da NYSC.

Kara karanta wannan

Sokoto: Tambuwal ya umarci a yi bincike kan kashe dalibar kwalejin da ta zagi Annabi

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng