2023: Zan soke JAMB, WAEC da NECO saboda kowa ya je makaranta inji ‘Dan takaran APC

2023: Zan soke JAMB, WAEC da NECO saboda kowa ya je makaranta inji ‘Dan takaran APC

  • Malam Adamu Garba II ya ce zai kawo tsare-tsaren da za su inganta harkar ilmi idan ya samu mulki
  • Matashin ya fito neman shugaban kasa a karkashin jam’iyyar APC, yana so ya yi takara a zaben 2023
  • Garba II ya yi alkawarin fatali da hukumomin jarrabawan da ake da su muddin ya karbi shugabanci

Lagos - Adamu Garba II wanda yana cikin masu neman takarar shugaban kasa a jam’iyyar APC, ya bayyana yadda zai bunkasa harkar ilmi a Najeriya.

Adamu Garba II ya yi bayani a shafinsa na Facebook, ya ce idan ya karbi mulkin kasar nan, zai ba kowa damar zuwa makarantu na gaba da sakandare.

Matashin ‘dan siyasar zai cin ma wannan buri ne ta hanyar ruguza hukumomin WAEC, NECO da JAMB da su ke shirya jarrabawan kammala sakandare.

Kara karanta wannan

Babu abin da zai hana PDP karbe mulkin Najeriya a 2023, In ji Ayu

Kamar yadda yake bayani, Garba II zai kawo tsari ta yadda duk wanda ya yi nasara a makarantun firamare da sakandare, zai iya zuwa mataki na gaba.

Manufar Adamu Garba II

“A cikin manufofinmu na sha’anin ilmi, za mu gyara jadawalin karatun firamare da sakandare, mu kashe WAEC, NECO da JAMB dukkansu.”

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

“Duk wani dalibin da ya kammala firamare da sakandare, zai samu damar zuwa makarantun gaba da sakandare kai-tsaye, a tsarin da muka zo da shi.”
'Dan takaran APC
Alhaji Adamu Garba II Hoto: @Adamu.garbaii
Asali: Facebook
“Makarantun sakandarenmu za su fi maida hankali ne wajen harkar horaswa da koyon sana’o’i.”

- Adamu Garba II

‘Dan takarar yana ganin hakan zai bunkasa harkar ilmi, ya rage nauyin da ke kan iyaye na kashe kudi, tare da cire ala-ka-kan da ake samu wajen karatu.

Malam Garba II a rubutun da ya yi, yake cewa hakkin kowane yaro ne a ilmantar da shi, ba gata ne.

Kara karanta wannan

Shirin 2023: Hadimin Buhari, Bashir Ahmad ya yi murabus daga kujerarsa

A wajen Garba II, hukumomin WAEC, NECO, JAMB, da NYSC duk su na tatsan jama’a ne babu gaira babu dalili, don haka yake da burin canza tsarin ilmi.

Za mu kawo CCSP - Garba II

Idan shugabanci ya fada hannun matashin, ya yi alkawarin kafa wata hukumar jarrabawa mai suna CCSP, wanda za ta rika gudanar da duk wata jarrabawa.

Ma’aiktar ilmi za ta lura da Hukumar CCSP wanda ita ce za ta shirya jarrabawar da za ta ba mutanen Najeriya damar yin karatu a jami’o’in kasashen waje.

Emefiele ya ajiye kujerarsa

Gwamnan jihar Ondo, Rotimi Akeredolu ya tsoma baki kan takarar da Godwin Emefiele yake shirin yi, ya bukaci Gwamnan nan CBN ya sauka daga kujerar da yake kai a yau.

Idan Emefiele ya ki yin murabus daga babban bankin kasar, Gwamnan ya ba shugaban kasa Muhammadu Buhari shawarar shige shi domin hakan ya saba doka.

Kara karanta wannan

Da duminsa: Bayan gaza biyan kudin Fam, Adamu Garba ya ce ya janye daga takara karkashin APC

Asali: Legit.ng

Online view pixel