Atiku ga 'yan Najeriya: Zan yi tsauri idan na karbi mulki daga hannun Buhari a 2023

Atiku ga 'yan Najeriya: Zan yi tsauri idan na karbi mulki daga hannun Buhari a 2023

  • Dan takarar shugaban kasa a Najeriya a inuwar PDP, Atiku Abubakar ya bayyana yadda mulkinsa zai kasance
  • Ya ce, zai tabbatar da tsauri wajen gudanar da aikinsa tare da tabbatar da doka da oda a kasar idan ya gaji Buhari
  • Ya kuma nemi goyon bayan al'ummar jihar Ondo, inda ya yaba musu bisa ba shi goyon baya a zaben 2019 da ya gabata

Akure, Ondo - Wani rahoton jaridar TheCable ya naqalto Atiku Abubakar, tsohon mataimakin shugaban kasa na cewa, zai yi tsauri wajen tabbatar da doka da oda idan aka zabe shi a matsayin shugaban kasa a zaben 2023.

Atiku, wanda ke fatan zama shugaban kasa a inuwar jam’iyyar PDP, ya yi magana ne a daren Lahadi a Akure yayin wani taron tattaunawa da wakilai da shugabannin jam’iyyar.

Kara karanta wannan

'Batanci: Atiku Ya Ce Ba Shine Ya Wallafa Rubutun Sukar Kashe Ɗalibar Sokoto a Shafinsa Ba

Yadda mulkin Atiku zai kasance a 2023
Atiku ga 'yan Najeriya: Idan kuka zabe ni a 2023, mulki na zai zama mai tsauri | Hoto: pmnewsnigeria.com

Ya ce zai dauki karin jami'ai a hukumomin tsaron kasar a wani bangare na kokarin yaki da rashin tsaro a kasar idan aka zabe shi a matsayin shugaban kasa, kamar yadda People Gazette ta ruwaito.

Ya kuma yi alkawarin kara sayo wa ‘yan sanda kayan aiki, inda ya kara da cewa samar da karin ma’aikata da kayan aiki ga hukumomin tsaro na daya daga cikin hanyoyin da za a bi wajen magance kalubalen tsaro da ake fuskanta.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ya kuma yabawa al’ummar jihar bisa yadda suka amince masa suka zabe shi a matsayin dan takarar jam’iyyar PDP a zaben 2019.

Ya bukaci wakilan jam'iyyar a jihar da su zabe shi a zaben fidda gwani na jam’iyyar da aka shirya yi a ranar 28 ga watan Mayu.

Da yake bayyana manufarsa, Atiku ya ce:

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Saraki ya bayyana alherin da ya tanadar wa 'yan Najeriya idan ya gaji Buhari

“Abu na farko shi ne hada kan al’ummar kasar nan. Ta yaya zan hada kan al’ummar kasar nan? Zan yi adalci ga kowane bangare na kasar nan.”

Tsohon mataimakin shugaban kasar ya kuma ce zai samar da isassun kudade ga bangaren ilimi, yana mai cewa "ilimi mabudin komai ne".

Da yake mayar da martani ga bukatun Atiku, Fatai Adams, shugaban PDP na jihar Ondo, ya tabbatar wa Atiku cewa wakilan PDP a jihar za su "saka masa" ta hanyar ba shi kuri'unsu.

Atiku Abubakar: Ni nake da gogewar da kwarewar iya dakile matsalar tsaro a Najeriya

A wani labarin, tsohon mataimakin shugaban kasa kuma dan takarar shugaban kasa a PDP, Abubakar Atiku, ya roki wakila da jiga-jigan jam’iyyar PDP a jihar Osun da su mara masa baya domin cimma manufarsa ta siyasa.

Atiku ya kuma bayyana musu irin gogewar da yake ita, inda yace shi ne zai iya kawar da matsalolin da kasar nan ke fuskanta, musamman na tsaro.

Kara karanta wannan

Babu abin da zai hana PDP karbe mulkin Najeriya a 2023, In ji Ayu

Hakazalika, ya ce yana da gogewar da ta dace wajen hada kan Najeriya da kawo sauyin fasali mai dorewa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.