Atiku Abubakar: Ni nake da gogewa da kwarewar iya dakile matsalar tsaro a Najeriya

Atiku Abubakar: Ni nake da gogewa da kwarewar iya dakile matsalar tsaro a Najeriya

  • Dan takarar shugaban kasa a jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar ya magantu kan yiwuwar magance matsalar tsaro
  • Ya ce, shi ne yake da gogewa duk cikin 'yan takara, ta yadda zai magance matsalolin Najeriya cikin sauki
  • Ya kuma hango matsala game da zaben jihar Osun mai zuwa, inda ya yi gargadin watakila PDP ta yi rashi

Osun - Tsohon mataimakin shugaban kasa kuma dan takarar shugaban kasa a PDP, Abubakar Atiku, ya roki wakilai da jiga-jigan jam’iyyar PDP a jihar Osun da su mara masa baya domin cimma manufarsa ta siyasa.

Atiku ya kuma bayyana musu irin gogewar da yake da ita, inda yace shi ne zai iya kawar da matsalolin da kasar nan ke fuskanta, musamman na tsaro.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Saraki ya bayyana alherin da ya tanadar wa 'yan Najeriya idan ya gaji Buhari

Hakazalika, ya ce yana da gogewar da ta dace wajen hada kan Najeriya da kawo sauyin fasali mai dorewa.

Alwashin Atiku wajen kawo karshen matsalar tsaro
Atiku Abubakar: Ni nake da gogewar da kwarewar iya dakile matsalar tsaro a Najeriya | Hoto: pmnewsnigeria.com

Ya koka kan matsalar rashin tsaro da kasar nan ke ciki, amma cikin sauri ya ce zai sadaukar da kansa ne don yiwa kasa hidima, inji rahoton Tribune Online.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A cewarsa:

“Ina da kwarewar da ta dace don tunkarar kalubalen Najeriya na rashin tsaro da rashin hadin kai. A lokacin da gwamnatinmu karkashin jagorancin Olusegun Obasanjo ta hau karagar mulki, mun fuskanci kalubale irin wannan kuma mun iya magance shi. Idan na zama shugaban kasa, zan tabbatar da sake fasalin kasar nan.”

PDP za ta iya rasa kujerar gwamna a Osun - Atiku

Atiku ya yi gargadin cewa jam’iyyar PDP za ta iya samun rashin nasara a zaben gwamnan jihar Osun mai zuwa nan kusa, inji rahoton The Nation.

Kara karanta wannan

2023: Moghalu Ya Lale N25m Ya Biya Kuɗin Fom Ɗin Takarar Shugaban Ƙasa a Jam'iyyarsa

Dan takarar shugaban kasan, a wata ziyara ya gana da tsohon gwamna Prince Olagunsoye Oyinlola da dan takarar jam’iyyar PDP na bangaren Sanata Ademola Adeleke a gidajensu kafin ya ziyarci ‘yan jam’iyyar a sakatariyar PDP da ke unguwar Biket.

Da yake magana, yace:

“Akwai wani abin da ya dame ni game da jihar nan, Osun. A zaben da ya gabata rashin jituwa tsakanin PDP da PDP ne ya sa muka fadi zabe.
“Yanzu ma, muna fuskantar irin wannan rikici a 2022, daya daga cikin dalilan da ya sa na zo nan shi ne in yi kira ga hadin kanku gabanin zabe domin ku samu nasara, ko ta halin kaka.
“Kun ga abin da rashin hadin kai ya jawo a zaben da ya gabata kuma muka fadi. Kada mu sake maimaita kuskuren nan; Ina rokon ku shuwagabanni da jiga-jigan jam’iyya. Wannan zabe shi ne ginshikin babban zabe kuma yana da matukar muhimmanci.”

Kara karanta wannan

Yajin aikin ASUU: Daliban jami'a sun fusata, sun ba lakcarori da gwamnati wa'adi su bude jami'o'i

Ya bukaci shugaban kwamitin riko na jam’iyyar a Osun da ya bi shawarwarin, don hana jam’iyyar PDP rashin nasara a zaben gwamna mai zuwa.

Gwarzon Dimokradiyya: Za a karrama shugaba Buhari da babbar lambar yabo

A wani labarin, nan ba da jimawa ba za a karrama shugaban kasa Muhammadu Buhari da lambar yabo ta gwarzon dimokuradiyya, wanda majalisar ba da shawara ta jam’iyyu (IPAC) za ta ba shi.

Jaridar PM News ta ruwaito cewa, Engr. Yusuf Yabagi, shugaban jam'iyyar ADP kuma kodinetan IPAC ne ya sanar da hakan a ranar Talata 26 ga watan Afrilu yayin wata liyafar buda baki da Buhari a Abuja.

Yabagi ya ce za a karrama Buhari ne saboda sanya hannu a kan dokar zabe mai dumbun tarihi domin tana wakiltar sauyi da zai tabbatar da zaman lafiya da karbuwa da zabuka a kasar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel