Tashin Hankali: 'Yan bindiga sun zagaye gari a Katsina, sun kashe mutane da dama

Tashin Hankali: 'Yan bindiga sun zagaye gari a Katsina, sun kashe mutane da dama

  • Wasu yan bindiga sun yi nufin aikata mummunar ta'asa a kauyen Gurbin Magarya dake ƙaramar hukumar Jibiya a jihar Katsina
  • Bayanai sun nuna cewa yan ta'addan sun toshe hanyoyin fita daga kauyen suka kashe mutum uku kafin Sojoji su kara so
  • Mazauna yankin sun tabbatar da cewa Sojoji da Yan bijilanti sun nuna jajircewa matuka har suka samu nasarar dakile harin

Katsina - Wasu yan bindiga sun farmaki kauyen Gurbin Magarya da ke yankin ƙaramar hukumar Jibiya a jihar Katsina, inda suka kashe mutane uku suka jikkata wasu uku.

Premium Times ta rahoto cewa maharan sun kashe dabbobi da yawa mallakin mutane da ke rayuwa a ƙauyen.

Wasu majiyoyi daga ƙauyen sun nuna cewa yan bindiga sun kai farmaki ne da misalin ƙarfe 10:00 na dare kuma suka toshe kowace ƙofar shiga da fita a ƙauyen.

Kara karanta wannan

Dalibai mata na jami'o'i biyu a Arewa zasu fito tituna zanga-zanga tsirara kan yajin aikin ASUU

Daya daga cikin mutanen da suka jikkata a harin.
Tashin Hankali: 'Yan bindiga sun zagaye gari a Katsina, sun kashe mutane da dama Hoto: premiuntimesng.com
Asali: UGC

Halliru Haladu, wani mazaunin garin Jibiya, ya ce:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"Ba dan Azziƙin Sojoji da yan Bijilantin da ke zaune a kan hanyar zuwa ƙauyuka daga garin Jibiya ba, da yan ta'addan sun ci nasarar share ƙauyen baki ɗaya."
"Dakarun sojin da yan Bijilanti sun yi namijin kokari kuma sun nuna kwazo, sun yi nasarar fatattakar maharan, amma kafin su kai ɗauki an riga an kashe mutum uku."

Haladu ya bayyana sunayen mutanen da suka rasa rayuwarsu a harin da suka haɗa da Muntari Naqawuri, Surajo Salisu da Musa Hassan. Ya ce Mustapha Salisu, Basiru Abubakar da Muhammad Rabiu sun ji raunuka.

Wani shugaban matasa, Mustapha Kabir, ya ce ya rinƙa jiyo ƙarar harbe-harbe daga Jibiya lokacin da yan ta'addan suka kai harin.

Punch ta rahoto Ya ce:

"Wasu mutane da suka daɗe a waje ba su shiga gida ba sun gaya mana cewa sun ga yan bindigan lokacin da suka nufi ƙauyen Gurbin Magarya kafin lamarin ya faru."

Kara karanta wannan

Cikakken Labari: Wani Bam Ya Tashi a Masallaci Yayin da Mutane ke tsaka da Sallar Jumu'a

Wane matakin hukumar yan sanda ta ɗauka?

Mai magana da yawun rundunar yan sanda reshen jihar Katsina, Gambo Isa, bai ɗaga kira ko ya turo amsar sakonnin da aka tura masa ba ta wayar salula game da harin.

A wani labarin kuma kun ji cewa Wata Nakiya da yan ta'adda suka ɗana wa Sojoji ta koma kan su, ta musu mummunar ɓarna

Wani abun fashewa da yan ta'addan Boko Haram/ISWAP suka ɗana wa Sojojin Najeriya ya tashi da wata tawagar yan uwan su.

Bayanai sun nuna cewa yan ta'addan na kan hanyar dawowa daga kai farmakin sata lokacin da Nakiyar ta tashi da su, shida suka sheƙa barzahu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel