Mayakan Boko Haram/ISWAP 6 sun mutu yayin da Nakiyar da suka ɗana ta tashi da su a Borno

Mayakan Boko Haram/ISWAP 6 sun mutu yayin da Nakiyar da suka ɗana ta tashi da su a Borno

  • Wani abun fashewa da yan ta'addan Boko Haram/ISWAP suka ɗana wa Sojojin Najeriya ya tashi da wata tawagar yan uwan su
  • Bayanai sun nuna cewa yan ta'addan na kan hanyar dawowa daga kai farmakin sata lokacin da Nakiyar ta tashi da su, shida suka sheƙa barzahu
  • Wata majiya ta bayyana cewa yan ta'addan ba su ji daɗin abin da ya auku ba, haka suka kwashe gawarwakin su suka bar wurin

Borno - Aƙalla mayaƙan kungiyar ta'addanci Boko Haram/ISWAP guda shida ne suka mutu yayin da wata nakiya ta tashi da su a jihar Borno.

Wata majiya daga cikin rundunar sojin Najeriya ta bayyana cewa yan ta'addan sun dasa Nakiyar ne da nufin ɗana wa Dakarun soji tarko, amma sai ya koma kan su.

Jaridar Leadership ta tattaro cewa yan ta'addan sun gamu da ajalin su ne yayin suke hanyar dawowa daga wani farmakin sata da suka kai yankin ƙauyen Nguma a ƙaramar hukumar Biu dake jihar.

Kara karanta wannan

Dalibai mata na jami'o'i biyu a Arewa zasu fito tituna zanga-zanga tsirara kan yajin aikin ASUU

Taswirar jihar Borno a cikin Najeriya.
Mayakan Boko Haram/ISWAP 6 sun mutu yayin da Nakiyar da suka ɗana ta tashi da su a Borno Hoto: Channelstv.com
Asali: UGC

Wasu bayanai da masanin harkokin tsaro na yankin tafkin Chadi, Zagazola Makama, ya tattara ta hannun wata majiyar soji, ya ce yan ta'addan na kan motocin yaƙi uku da Mota ɗaya yayin da abun ya rutsa da su.

A cewarsa yayin da suke kan waɗan na motocin a hanyar komawarsu dai-dai mahaɗar Sabongari da Murte, ɗaya daga cikin motocin ta taka abun fashewar kuma ya tashi.

Majiyar Sojojin ta bayyana cewa wannan ƙaiƙayi da ya koma kan mashekiya ya laƙume rayukan 'yan ta'adda Shida, wasu da yawa suka jikkata.

"Nan take suka fusata da abun da ya auka musu, suka huce fushin su kan wani Makiyayi, matarsa da kuma ɗan sa, suka kashe su nan take." inji majiyar.

Bugu da ƙari majiyar ta ƙara da cewa yan ta'addan cikin fushi suka kwashi gawarwakin yan uwan su da suke kira 'Mujahideen' suka bar wurin.

Kara karanta wannan

Cikakken Labari: Wani Bam Ya Tashi a Masallaci Yayin da Mutane ke tsaka da Sallar Jumu'a

A wani labarin na daban kuma Wani Minista Buhari da Sanatan APC sun lale miliyan N200m sun sayi Fom ɗin takarar shugaban ƙasa

Tsohon gwamnan jihar Abia kuma Ministan kimiyya da fasaha, Ogbonnaya Onu, ya karbi Fom din nuna sha'awa da tsayawa takarar shugaban ƙasa na APC kan kuɗi miliyan N100m.

Jaridar Vanguard ta rahoto cewa Sanatan APC kuma tsohon gwamnan jihar Ogun, Sanata Ibikunle Amosun , ya bi sahun saura, ya sayi Fom ɗin takara yau Jumu'a.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

Online view pixel