Da Dumi-Dumi: Wani Bam Ya Tashi a Masallaci Musulmai na tsaka da Sallar Jumu'a

Da Dumi-Dumi: Wani Bam Ya Tashi a Masallaci Musulmai na tsaka da Sallar Jumu'a

  • Wani Bam ya tashi da Musulmai yayin da suke cikin bautar Allah a Masallacin Jumu'a a birnin Kabul na ƙasar Afghanistan
  • Hukumar yan sandan ƙasar ta ce a rahoton da ta tattara na farko mutum uku sun mutu yayin da wasu da dama suka jikkata
  • Sai dai wata majiya daga yankin Masallacin ta nuna cewa adadin mutanen da abun ya shafa ya zarce haka

Aƙalla mabiya addinin Musulunci uku ne suka rasu yayin da wani Bam ya tashi a Masallaci a Kabul ranar Jumu'a, a cewar hukumar yan sandan ƙasar Afghanistan.

Kakakin hukumar yan sandan, Khalid Zadran, yace tashin Bam ɗin ya nuna Masallatan aka nufa a Masallacin Ayoub-e-Saber,, kamar yadda Jaridar Punch ta rahoto.

Taswirar ƙasar Afghanistan.
Da Dumi-Dumi: Wani Bam Ya Tashi a Masallaci Musulmai na tsaka da Sallar Jumu'a Hoto: punchng.com
Asali: UGC

Ya ƙara da cewa bayanan farko ne suka nuna wannan dadin na mutanen da suka mutu amma wata majiya daga yankin ta ce adadin waɗan da abun ya shafa ya zarce haka.

Kara karanta wannan

Kai tsaye: Shugaba Buhari na zaman bankwana da Ministocinsa da sukayi murabus

Karin bayanai har da musabbabin da ya hadddasa tashin Bam ɗin zuwa yanzun ba'a gano ba amma hukumomi na iya bakin kokarin su.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ƙasar Afghanistan na cigaba da fuskantar ƙaruwar hare-hare irin waɗan nan, amma ƙungiyar IS ke kan gaba wajen ayyana cewa ita ce ta ɗauki nauyin kai hari a lokuta da dama.

A yan watannin nan da suka shuɗe, sama da mutane 1,000 ne suka rasa rayukan su a jerin hare-haren da aka kai Masallatai, kananan addinai da kuma makaranta.

A wani labarin na daban kuma Wani Bam ya sake tashi a gidan giya a jihar Kogi, mutane sun mutu

Wani abun fashewa da mutane ke zaton Bam ne ya tashi a wata mashaya da ke Kabba, jihar Kogi ranar Laraba da daddare.

Wasu mazauna yankin da suka garzaya wurin gane wa ido sun ce mutum uku ne suka mutu wasu kuma na kwance a Asibiti.

Kara karanta wannan

Gara ku biya kuɗin fansar Fasinjojin jirgin kasa da ku sayi Fom ɗin takara a 2023, Sheikh Gumi

Asali: Legit.ng

Online view pixel