'Yan bindiga sun halaka sama da mutane 50 a wani sabon mummunan hari a Zamfara

'Yan bindiga sun halaka sama da mutane 50 a wani sabon mummunan hari a Zamfara

  • Yan bindiga sun sake kaddamar da wasu hare-haren ta'addanci kan al'umma a jihar Zamfara a ƙarshen makon nan
  • Bayanai sun nuna cewa yan ta'addan sun ƙashe akalla mutum 55 a yankunan kananan hukumomi biyu na jihar
  • Har zuwa yanzun hukumar yan sandan reshen jihar ba tace uffan ba kan lamarin da suka faru

Zamfara - Aƙalla mutane 55 aka tabbatar sun rasa rayukansu a wasu sabbin hare-hare biyu da yan bindiga suka kai yankunan kananan hukumomi biyu a Zamfara.

Vanguard ta rahoto cewa kusan mutum 48 yan ta'addan suka kashe a ƙauyukan Sabon Garin Damri, Damri da Kalahe a ƙaramar hukumar Bakura.

Shugaban dake kula da yankin Bakura, Aminu Suleiman, wanda ya tabbatar da faruwar lamarin a ƙarshen makon nan, ya ce yan bindigan sun shiga Sabon Gari da misalin ƙarfe 2:00 na rana ranar Jumu'a.

Kara karanta wannan

Cikakken Labari: Wani Bam Ya Tashi a Masallaci Yayin da Mutane ke tsaka da Sallar Jumu'a

Yan ta'adda sun sake mai hari Zamfara.
'Yan bindiga sun halaka sama da mutane 50 a wani sabon mummunan hari a Zamfara Hoto: channelstv.com
Asali: UGC

Rahoto ya nuna sun ƙashe mutane 9 a nan, kuma suka wuce garin Damri, inda suka yi ajalin wasu mutum huɗu ciki har da ɗan sanda da jami'in hukumar NSCDC.

Haka nan yan ta'addan waɗan da suka kai hari kan babura da yawa sun kona Motar Hilux mallakin yan sanda.

Bayan haka maharan sun ƙara kashe mutum 8 a ƙauyen Kalahe, wanda ke tsakanin Sabon Garin Damri da kuma cikin garin Damri.

A cewar Sulaiman yan bindigan ba su tsaya nan ba, sun farmaki Asibitin da ake duba marasa lafiya kuma suka kashe majinyata.

Wane mataki jami'an tsaro suka ɗauka?

Sulaiman ya ƙara da cewa Dakarun Sojoji sun tari yan ta'addan a yankin Damri aka yi musayar wuta, wanda hakan ya tilasta musu tserewa zuwa Sabon Garin Damri, inda suka yi ajalin wasu 21.

Kara karanta wannan

Gara ku biya kuɗin fansar Fasinjojin jirgin kasa da ku sayi Fom ɗin takara a 2023, Sheikh Gumi

Ya ce:

"Sojoji sun shiga garin suka yi musayar wuta da yan bindiga, bisa tilas suka sake koma wa Sabon Garin Damri bayan ƙashe mutum 9 da farko, suka koma suka ga bayan wasu 21."

Shugaban yankin ya tabbatar da cewa a dukkan hare-haren aƙalla mutane 48 ne suka rasa rayukansu.

Yan bindiga sun sake kai sabon hari

A wani sabon harin kuma ranar Asabar, wata majiya daga yankin Maradun ta bayyana cewa an sake kai hari kauyukan Faru da Minane, kamar yadda Channels tv ta ruwaito.

"Ina cikin babban Asibitin Maradun lokacin da sojoji suka kawo gawarwakin mutanen da aka kashe," inji wani Jamilu Muhammad.

"Mutanen mu a kauyen Minane sun ce yan ta'adda sun shigo mintuna kafin ƙarfe biyu na rana, suka buɗe wuta kan mai uwa da wabi."

A cewarsa, mutum shida aka kashe a kauyen Minane yayin da wani mutum ɗaya ya mutu a Faru. Ya ce adadin mutanen da suka mutu zasu iya ƙaruwa saboda mutane da dama sun bata.

Kara karanta wannan

Wani Bam ya ƙara tashi mutane na tsaka da holewa a jihar Kogi, rayuka sun salwanta

Kakakin rundunar yan sanda reshen jihar Zamfara, Mohammed Shehu, be amsa kira ko sakonnnin da aka tura masa ta wayar salula ba.

A wani labarin kuma Wata Nakiya da yan ta'adda suka ɗana wa Sojoji ta koma kan su, ta musu mummunar ɓarna a Borno

Wani abun fashewa da yan ta'addan Boko Haram/ISWAP suka ɗana wa Sojojin Najeriya ya tashi da wata tawagar yan uwan su.

Bayanai sun nuna cewa yan ta'addan na kan hanyar dawowa daga kai farmakin sata lokacin da Nakiyar ta tashi da su, shida suka sheƙa barzahu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel