Abuja-Kaduna: Gara ku biya kuɗin fansar Fasinjojin jirgin kasa da ku sayi Fom ɗin takara, Sheikh Gumi

Abuja-Kaduna: Gara ku biya kuɗin fansar Fasinjojin jirgin kasa da ku sayi Fom ɗin takara, Sheikh Gumi

  • Sheikh Dakta Ahmad Gumi ya shawarci gwamnatin Buhari ta biya bukatun yan ta'adda don kubutar da mutanen da suka sace a jirgin ƙasa
  • Fitaccen Malamin ya ce maimakon taimakawa talakawan da ba zasu iya biyan fansa baa shugabanni sun gwammace su sayi Fom
  • A wurin taron Addu'a na musamman don kubutar Fasinjojin, shugaban CAN a Kaduna ya ƙalubalanci shugabanni

Kaduna - Shaharren Malamin addinin musulunci, Sheikh Ahmad Gumi, ya shawarci gwamnatin tarayya ta biya yan ta'addan da suka sace Fasinjoji 62 a jirgin kasa kuɗin fansa.

Malamin ya ba da wannan shawarin ne a wurin taron Addu'a ta musamman domin kuɓutar Fasinjojin wanda Jam'iyyar Matan Arewa (JMA) ta shirya a Kaduna ranar Alhamis.

Daily trust ta ruwaito cewa a ranar 28 ga watan Maris ne yan bindiga suka farmaki jirgin inda suka kashe mutum 9 kuma suka sace wasu 62.

Kara karanta wannan

Cikakken Labari: Wani Bam Ya Tashi a Masallaci Yayin da Mutane ke tsaka da Sallar Jumu'a

Sheikh Ahmad Gumi.
Abuja-Kaduna: Gara ku biya kuɗin fansar Fasinjojin jirgin kasa da ku sayi Fom ɗin takara, Sheikh Gumi Hoto: dailytrust.com
Asali: Facebook

Punch ta rahoto a jawabinsa, Dakta Gumi ya ce:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"Duba yadda mutane suka biya kuɗin Fom ɗin takara kusan biliyan N25bn maimakon su yi amfani da kuɗin su biya kuɗin fansar talakawan Najeriya waɗan da ba zasu iya biya ba."
"Duk abin da suke bukata (yan ta'adda) ku ba su saboda mutanen nan su kuɓuta, bayan sun sako su ku na da yancin ɗaukar mataki a kan su."
"Daga nan kun samu cikakkiyar damar yaƙar su yadda ya dace saboda idan suna rike da mutane dole ku bi a hankali don gudun ka da waɗan da ba ruwan su su cutu."

A nashi jawabin shugaban kungiyar kiristoci CAN a Kaduna, Rabaran Joseph Hayab, ya kalubalanci shugabanni su yi abin da ya dace don tabbatar da Fasinjojin sun kuɓuta cikin koshin lafiya.

Meyasa JMA ta shirya taron Adddu'a?

Kara karanta wannan

2023: Igbo Ba Abin Yarda Bane, Ba Mu Amince Su Mulki Ƙasa Ba, Ƙungiyoyin Arewa

Shugabar JMA, Hajiya Rabi Musa Saulawa, ta ce ƙungiyarsu ta shirya taron Addu'ar ne domin rokon Allah ya kubutar da Fasinjojin cikin koshin lafiya da kuma dawo da zaman lafiya a ƙasa.

Legit.ng Hausa ta tattaro cewa taron Addu'ar ya sami halartar Malaman Musulunci da kuma na kiristanci.

A wani labarin kuma Hukumar sojojin Najeriya ta kama wani Soja dake siyarwa yan bindiga makamai a Zamfara

Hukumar sojojin Najeriya ta kama wani Soja dake sayarwa yan bindiga makamai da kayan sojoji a jihar Zamfara.

Rahotanni sun bayyana cewa an kama sojan ne yana shirin sayar da Alburusai 1,000 kan kudi Naira miliyan ɗaya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel