JTF sun halaka 'yan bindiga 10 a Niger bayan sun yi yunkurin hargitsa shagalin sallah

JTF sun halaka 'yan bindiga 10 a Niger bayan sun yi yunkurin hargitsa shagalin sallah

  • Jami'an tsaron hadin guiwa sun sheke a kalla 'yan bindiga goma, yayin da suka yi yunkurin tarwatsa shagalin bikin sallar karama a karamar hukumar Rafi ta jihar Neja
  • Kwamishinan kananan hukumomi, Emmanuel Umar ne ya tabbatar da aukuwar lamarin jiya, tare da bayyana yadda hatsabiban suka kai hari kauyen Kawo da Uregi a ranar Litinin
  • Tsananin ragargaza ce ta sanya su tserewa, gami da barin babura 7 dauke da miyagun makamai, bayan an sheke 10 daga cikinsu tare da ceto mutum 14 da aka yi garkuwan dasu

Niger - Jami'an tsaro sun sheke a kalla 'yan bindiga guda goma yayin da suka yi yunkurin tarwatsa shagalin bikin sallar azumi a karamar hukumar Rafi ta jihar Neja.

Kwamishinan kananan hukumomi, Emmanuel Umar ne ya tabbatar da aukuwar lamarin jiya, jaridar The Nation ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Sokoto: Bishop Kukah ya yi martani kan kashe dalibar da ta yi batanci ga Annabi

JTF sun halaka 'yan bindiga 10 a Niger bayan sun yi yunkurin hargitsa shagalin sallah
JTF sun halaka 'yan bindiga 10 a Niger bayan sun yi yunkurin hargitsa shagalin sallah. Hoto daga dailytrust.com
Asali: UGC

Ya ce, 'yan bindiga sun kai hari kauyen Kawo da Uregi a ranar Litinin ana tsaka da shagalin bikin karamar sallah.

A cewarsa, jami'an tsaron hadin guiwa ne suka ceto wadanda aka yi garkuwan dasu guda 14, tare da kwace babura bakwai na miyagun 'yan ta'addan.

The Cable ta ruwaito cewa, jami'an tsaron sun yi hanzarin dakile harin, gami da isa wurin da hatsabiban ke cin karensu babu babbaka a wuraren Uregi da kauyukan Kiribo.

"An sheke kusan goma daga cikin 'yan bindigan, sannan aka kwato wadanda aka yi garkuwan dasu har mutum 14, tare da babura bakwai dauke da makamai."

Sheikh Gumi ya kafa kungiyar kare hakkin Fulani Makiyaya

A wani labari na daban, Fitaccen malamin addinin Musulunci, Ahmad Gumi, ya sanar da cewa ya kafa kungiyar assasa kare hakkin Fulani makiyaya.

Kara karanta wannan

Sokoto: An kama wadanda suka kashe dalibar da ake zargin ta zagi Annabi

Gumi ya bada sanarwan kafa kungiyar wacce za a kira ta da Nomadic Rights Concern (NORIC) a yayin tafsirin watan Ramadan a Masallacin Sultan Bello da ke Kaduna.

Ya ce kungiyar za ta tattaro tare da bayyana irin cin zarafi da take hakkokin Fulani makiyaya da ake yi, Premium Times ta ruwaito.

"Mun ga dacewar kafa Kungiyar Kula da Hakkokin Makiyaya, NORIC, wacce za ta samu shugabancin Farfesa Umar Labbo. NORIC za ta zama wata hanya da makiyaya za su mika korafinsu da damuwarsu zuwa ga hukumomin da suka dace."

Asali: Legit.ng

Online view pixel