Jama'ar gari sun kadu da ganin makwabcinsu a cikin yan bindigar da suka farmake su

Jama'ar gari sun kadu da ganin makwabcinsu a cikin yan bindigar da suka farmake su

  • Al'ummar garin Takakume a karamar hukumar Goronyo da ke jihar Sokoto sun cika da fargaba bayan ganin makwabcinsu a cikin yan bindigar da suka farmake su
  • Maharan dai sun farmaki garin ne a safiyar yau Lahadi inda suka fafata da yan bindiga lamarin da ya kai ga kisan shugaban yan bindigar
  • Shugaban Karamar Hukumar Goronyo, Malam Abdulwahab, ya ce ’yan bindigar sun kai hari tare da yin ajalin wani bawan Allah sannan suka yi awon gaba da wasu mutane shida

Sokoto - Mazauna garin Takakume a karamar hukumar Goronyo da ke jihar Sokoto sun kadu a ranar Lahadi lokacin da suka gano cewa tsohon makwabcinsu ne shugaban yan bindigar da suka farmake su.

Yan bindiga dauke da makamai sun farmaki garin a safiyar ranar Lahadi, amma sai yan banga suka yi musayar wuta da su, lamarin da ya yi sanadiyar mutuwar shugaban yan ta’addan, rahoton Daily Trust.

Kara karanta wannan

Ta'addanci: 'Yan ta'adda sun bindige jami'an 'yan sanda har 3 a jihar Neja

Jama'ar gari sun kadu da ganin makwabcinsu a cikin yan bindigar da suka farmake su
Jama'ar gari sun kadu da ganin makwabcinsu a cikin yan bindigar da suka farmake su Hoto: channelstv.com
Asali: UGC

Wani mazaunin garin da ya nemi a sakaya sunansa ya ce:

“Shine ya jagoranci harin da aka kai garin.”

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Da yake zantawa da manema labarai, shugaban karamar hukumar, Abdulwahab Goronyo, ya ce yan bindigar sun farmaki garin da tsakar dare, suka kashe mutum daya tare da sace wasu shida.

Ya ce:

“Yan banga a yankin sun fatattaki yan bindigar sannan a cikin haka sai suka kashe daya daga cikinsu wanda daga baya aka gano yana daya daga cikin mutanen da suka taba zama a yankin. Ya zauna tare da iyayensa.”

Shugaban karamar hukumar ya kara da cewa yan bindiga sun farmakin wannan kauyen yan kwanaki da suka gabata, yayin da wadanda aka sace ke a hannunsu har yanzu.

Sai dai wata majiya kuma ta ce bakin cikin an kashe wa ’yan bindigar jagoransu ne ya sanya suka harbe mutanen da suka yi awon gaba da su, Aminiya ta rahoto.

Kara karanta wannan

Sokoto: Tambuwal ya umarci a yi bincike kan kashe dalibar kwalejin da ta zagi Annabi

Majiyar ta ce:

“Yan bindigar sun harbe mutanen da suka sace, kuma da safiyar yau muka kwaso gawawwakinsu aka yi musu janaiza.”

Matsalar tsaron Najeriya akwai siyasa ciki, Farfesa Yemi Osinbajo

A wani labarin, mataimakin shugaban kasa kuma mai niyyar takara kujeran shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo, ya bayyana cewa akwai siyasa da yawa cikin lamarin tsaro a kasar nan.

Osinbajo ya bayyana hakan ne yayin tattaunawa da deleget din jiha Anambra yayinda ake shirin zaben tsayar da gwamni na jam'iyyar APC.

A cewarsa, sayo makamai na daukan dogon lokaci kuma gwamnatinsu na odan makamai daga Amurka da kasashen Turai, rahoton Vanguard.

Asali: Legit.ng

Online view pixel