Matsalar tsaron Najeriya akwai siyasa ciki, Farfesa Yemi Osinbajo

Matsalar tsaron Najeriya akwai siyasa ciki, Farfesa Yemi Osinbajo

  • Farfesa Yemi Osinbajo ya bayyana cewa gwamnatin Buhari na iyakan kokarinta wajen magance matsalar tsaro
  • Osinbajo yace akwai masu siyasantar da matsalar tsaron amma suna kokari yadda ya kamata
  • Mataimakin shugaban kasa yace aiki ya yiwa Sojoji, yan sanda da sauran hukumomin tsaro yawa

Enugu - Mataimakin shugaban kasa kuma mai niyyar takara kujeran shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo, ya bayyana cewa akwai siyasa da yawa cikin lamarin tsaro a kasar nan.

Osinbajo ya bayyana hakan ne yayin tattaunawa da deleget din jiha Anambra yayinda ake shirin zaben tsayar da gwamni na jam'iyyar APC.

A cewarsa, sayo makamai na daukan dogon lokaci kuma gwamnatinsu na odan makamai daga Amurka da kasashen Turai, rahoton Vanguard.

Yace:

"Muna kawar da matsalar tsaro a Arewa maso gabas, hakazalika Arewa maso yamma. Kuma muna magance rikice-rikicen dake aukuwa a ko ina, wanda ya hada da Kudu maso gabas da Kudu maso kudu."

Kara karanta wannan

Sabon salo: Birkitaccen mawaki ya fito takarar gaje Buhari a jam'iyyun siyasa har biyu

"A karon farko, aiki ya yiwa hukumomin tsaro yawa...Ban tunanin wata gwamnati ta taba adadin zaman majalisar tsaro kamar yadda gwamnatinmu tayi."

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"Muna bukatan karin jami'an tsaro saboda haka sai an yi sabon dauka da kuma sayo makamai."

Farfesa Yemi Osinbajo
Matsalar tsaron Najeriya akwai siyasa ciki, Farfesa Yemi Osinbajo Hoto: Presidency
Asali: Twitter

Karon farko tun bayan ayyana niyyar takara, Osinbajo da Tinubu sun hadu a zaman hadin kai

Karon farko tun bayan ayyana niyyar takara kujeran shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo, ya yi ido hudu da maigidansa, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu a jihar Legas.

Manyan jigogin APCn biyu sun hadu ne a taron zaman hadin kai tsakanin yan takara kujeran shugaban kasa karkashin jam'iyyar APC daga yankin kabilar Yoruba.

Dattawan yankin kudu maso yamma ne suka shirya zaman don ganin yadda za'a hada kai da juna don tsayar da mutum guda cikinsu.

Kara karanta wannan

A hukumance: Jita-jita ta kare, Saraki ya bayyana tsayawa takara, ya fadi dalilai

Dattawan sun hada da tsohon gwamnan jihar Osun, Cif Bisi Akande, da tsohon gwamnan jihar Ogun, Cif Olusegun Osoba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel