Wani Minista Buhari da Sanatan APC sun lale miliyan N200m sun sayi Fom ɗin takarar shugaban ƙasa

Wani Minista Buhari da Sanatan APC sun lale miliyan N200m sun sayi Fom ɗin takarar shugaban ƙasa

  • Ministan kimiyya da Fasaha, Ogbonnaya Onu, ya sayi Fom ɗin takarar shugaban ƙasa a APC, ya ce shi mutum ne mai tausayi
  • Duk a ranar Jumu'a tsohon gwamnan Ogun kuma Sanata mai ci, Ibikunle Amosun, ya lale nashi kuɗin ya karbi Fom
  • Jam'iyyar APC ta kama hanyar tara makudan kudi a siyar da Fom ɗin takarar shugaban ƙasa kaɗai

Abuja - Tsohon gwamnan jihar Abia kuma Ministan kimiyya da fasaha, Ogbonnaya Onu, ya karbi Fom din nuna sha'awa da tsayawa takarar shugaban ƙasa na APC kan kuɗi miliyan N100m.

Jaridar Vanguard ta rahoto cewa Sanatan APC kuma tsohon gwamnan jihar Ogun, Sanata Ibikunle Amosun, ya bi sahun saura, ya sayi Fom ɗin takara yau Jumu'a.

Minista Onu da Sanata Amosun.
Da Dumi-Dumi: Wasu Ministocin Buhari guda biyu sun sayi Fom ɗin takarar shugaban ƙasa Hoto: thecable.ng
Asali: UGC

Haka nan kuma, Abokai makusantan gwamnan babban bankin Najeriya (CBN), Godwin Emefiele, sun saya masa Fom ɗin takarar kujera lamba ɗaya a ƙasar nan.

Kara karanta wannan

Kwankwaso da wasu manyan jiga-jigan APC sun dira filin Malam Aminu Kano

Sun lale kudin sun karɓi Fom ɗin a madadin gwamnan CBN da misalin ƙarfe 11:15 na safiyar yau Jumu'a kamar yadda rahotanni suka nuna.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Yan takara dake hangen kujerar shugaban kasa, Muhammadu Buhari, a jam'iyyar APC na cigaba da ƙara tabbatar da aniyarsu ta hnayar lale N100m na Fom.

Tuni dai jagoran jam'iyya mai mulki na ƙasa, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, ya karɓi na shi Fom ɗin a kan waɗan nan makudan kuɗaɗe.

Haka nan kuma, Mataimakin shugaban ƙasa, Farfesa Yemi Osinbajo, wanda ake kallon yaron Tinubu ne a siyasa, ya karɓi na shi Fom ɗin tsayawa takara.

Legit.ng Hausa ta tattaro cewa masu yunkurin gaje Buhari a APC kaɗai sun haura mutum 20, da yuwuwar jam'iyya mai mulki tara sama da biliyan biyu na Fom.

A wani labarin na daban kuma Wani Bam da yan ta'adda suka ɗana wa Sojoji ya koma kan su, ya musu mummunar ɓarna

Kara karanta wannan

Da Duminsa: Goodluck Jonathan ba zai yi takarar shugaban kasa a jam'iyyar APC ba

Wani abun fashewa da yan ta'addan Boko Haram/ISWAP suka ɗana wa Sojojin Najeriya ya tashi da wata tawagar yan uwan su.

Bayanai sun nuna cewa yan ta'addan na kan hanyar dawowa daga kai farmakin sata lokacin da Nakiyar ta tashi da su, shida suka sheƙa barzahu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel