Ba zan sa a sake Kanu ba: Buhari ya yi watsi da bukatar shugabannin Igbo

Ba zan sa a sake Kanu ba: Buhari ya yi watsi da bukatar shugabannin Igbo

  • Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi watsi da bukatar shugabannin Igbo kan batun sakin Nnamdi Kanu
  • A yau ne shugaban ya gana da shugabannin yankin Kudu, inda suka bijiro da batutuwa da suka shafi yankin ciki har da na Kanu
  • Shugaba Buhari ya ce kamata ya yi a bar kotu ta bayyana adalcinta kan Nnamdi Kanu domin ganin yadda za ta kaya

Ebonyi - Shugaban kasa Muhammadu Buhari, a ranar Juma’a ya yi kira ga shugabannin Kudu-maso-Gabas da su kyale shari’ar da ake yi a kotu ta shugaban IPOB, Mazi Nnamdi Kanu a kasar.

Buhari ya bayyana haka ne a wata ganawa da ya yi da shugabannin yankin Kudu maso Gabas da suka hada da shugabannin kungiyar Ohanaeze Ndigbo a sabon gidan gwamnati da ke Abakaliki, Vanguard ta ruwaito.

Kara karanta wannan

'Batanci: Bayan Buhari Ya Yi Allah Wadai Da Kisan Deborah a Sokoto, Osinbajo Ya Yi Magana Da Kakkausar Murya

Martanin Buhari ga shugabannin Igbo kan rokonsu na a saki Nnamdi Kanu
Ba zan sa a sake Kanu ba: Buhari ya yi watsi da bukatar shugabannin Igbo | Hoto: premiumtimesng.com
Asali: UGC

Shugaban wanda ya kammala ziyarar aiki ta kwanaki biyu a jihar a yau Juma'a, ya yi nuni da cewa matakin da kotu ta dauka kan lamarin Kanu shi za a bi.

Buhari ya kuma nuna rashin jin dadinsa kan yadda ake ta fama da matsalar rashin tsaro a kasar, inda ya ce duk wanda da aka gani dauke da bindigar AK 47 a kowane yanki na kasar nan, to a yi masa kallon dan ta'adda matukar ba jami'in tsaro bane.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A bangare gudam ya kuma yabawa Gwamna David Umahi bisa ayyukan canza rayuwa da gwamnatin sa (Umahi) ta aiwatar, kamar yadda jaridar The Punch ta ruwaito.

Ka saki Nnamdi Kanu: Shugabannin Igbo sun kalli Buhari ido da ido, sun roki alfarma

A wani labarin, shugabannin yankin Kudu maso Gabas sun bukaci da a gaggauta sakin shugaban tsagerun IPOB, Nnamdi Kanu daga tsare shi da gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari ta yi.

Kara karanta wannan

2023: Igbo Ba Abin Yarda Bane, Ba Mu Amince Su Mulki Ƙasa Ba, Ƙungiyoyin Arewa

Shugabannin sun yi wannan roko ne a wata tattaunawa da suka yi da Buhari a zauren majalisar zartarwa da ke gidan gwamnati a Abakaliki, babban birnin jihar Ebonyi, inji rahoton Punch.

Buhari ya kai ziyarar aiki ta kwanaki biyu a jihar Ebonyi, kamar yadda rahotanni daga fadar shugaban kasa da gwamnatin Ebonyi ta bayyana, The Nation ta ruwaito.

Asali: Legit.ng

Online view pixel