Ka saki Nnamdi Kanu: Shugabannin Igbo sun kalli Buhari ido da ido, sun roki alfarma

Ka saki Nnamdi Kanu: Shugabannin Igbo sun kalli Buhari ido da ido, sun roki alfarma

  • Shugaban kasa Muhammadu Buahri ya kai ziyara jihar Ebonyi ya gana da shugabannin Igbo na yankin
  • Sun nemi ya yafewa shugaban 'yan aware Nnamdi Kanu ya sake shi, duk da cewa Kanu na fuskantar shari'a a kotu
  • A jiya ne shugaban ya isa garin, inda ya kaddamar da wasu ayyuka da gwamnatin jihar Ebonyi ta yi

Ebonyi - Shugabannin yankin Kudu maso Gabas sun bukaci da a gaggauta sakin shugaban tsagerun IPOB, Nnamdi Kanu daga tsare shi da gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari ta yi.

Shugabannin sun yi wannan roko ne a wata tattaunawa da suka yi da Buhari a zauren majalisar zartarwa da ke gidan gwamnati a Abakaliki, babban birnin jihar Ebonyi, inji rahoton Punch.

An roki Buhari ya sake Nnamdi Kanu
Ka saki Nnamdi Kanu: Shugabannin Igbo sun kalli Buhari ido da ido, sun roki alfarma | Hoto: premiumtimesng.com
Asali: UGC

Buhari ya kai ziyarar aiki ta kwanaki biyu a jihar Ebonyi, kamar yadda rahotanni daga fadar shugaban kasa da gwamnatin Ebonyi ta bayyana, The Nation ta ruwaito.

Kara karanta wannan

'Batanci: Bayan Buhari Ya Yi Allah Wadai Da Kisan Deborah a Sokoto, Osinbajo Ya Yi Magana Da Kakkausar Murya

Shugaban Majalisar Sarakunan Gargajiya na Kudu maso Gabas, Eze Charles Mkpuma ne ya karanta jawabin nema wa Kanu afuwa.

Ya ce:

"Muna rokon ka da ka yi adalci da jin kai ga dan mu Nnamdi Kanu."

Shugaba Buhari ya dura Enugu, zai zarce Ebonyi ziyarar aiki ta kwana biyu

A jiya Alhamis, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sauka a filin jirgin sama na Alamo Ibiam na jihar Enugu, inda zai zarce zuwa jihar Ebonyi.

Jirgin shugaban kasar ya isa Enugu ne da misalin karfe 10:30 na dare, The Nation ta ruwaito.

Gwamnan Enugu Ifeanyi Ugwuanyi da takwaransa na Ebonyi David Umahi da sauran jami’an gwamnati sun tarbe shi.

Shugaban ya kai ziyarar aiki ne ta kwanaki biyu a jihar Ebonyi inda ake sa ran zai kaddamar da ayyuka da dama da gwamnatin Umahi ta aiwatar.

Kara karanta wannan

Shirin 2023: Buhari fa na da dan takarar da yake so ya gaje shi, Adesina ya magantu

Gwarzon Dimokradiyya: Za a karrama shugaba Buhari da babbar lambar yabo

A wani labarin, nan ba da jimawa ba za a karrama shugaban kasa Muhammadu Buhari da lambar yabo ta gwarzon dimokuradiyya, wanda majalisar ba da shawara ta jam’iyyu (IPAC) za ta ba shi.

Jaridar PM News ta ruwaito cewa, Engr. Yusuf Yabagi, shugaban jam'iyyar ADP kuma kodinetan IPAC ne ya sanar da hakan a ranar Talata 26 ga watan Afrilu yayin wata liyafar buda baki da Buhari a Abuja.

Yabagi ya ce za a karrama Buhari ne saboda sanya hannu a kan dokar zabe mai dumbun tarihi domin tana wakiltar sauyi da zai tabbatar da zaman lafiya da karbuwa da zabuka a kasar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel