Sojoji sun sheke 'yan IPOB 4 da ke tilasta dokar hana fita ta kin jinin Buhari a Kudu

Sojoji sun sheke 'yan IPOB 4 da ke tilasta dokar hana fita ta kin jinin Buhari a Kudu

  • 'Yan ta'adda da ke tada hankali saboda fafutukar kafa kasar Biafra sun gama da gamonsu, sojoji sun ragargaje su
  • An hallaka wasu 'yan ta'adda da ke barazana ga mazauna yankin da sunan kakaba wata haramtancciyar dokar hana fita
  • ‘Yan bindigar sun yi arangama da sojojin da ke bataliya ta 144 na biregediya 14 na sojojin Najeriya, sun kuma gane banmbancin

jihar Abia - Rahoton jaridar Punch na nuni da cewa sojojin bataliya ta 144 na birged 14 na Najeriya sun hallaka wasu ‘yan ta'adda kusan hudu a ranar Laraba 4 ga watan Mayu a birnin kasuwanci na Aba na jihar Abia.

A cewar rahoton, lamarin ya faru ne da misalin karfe biyu na ranar a unguwar Uratta dake Aba a hanyar Enugu zuwa Fatakwal.

Kara karanta wannan

Ta'addanci: 'Yan ta'adda sun bindige jami'an 'yan sanda har 3 a jihar Neja

'Yan IPOB sun gamu da fushin soja a jihar Abia
Sojoji sun sheke 'yan IPOB da ke tursasa wa jama'a zaman gida a jihar Abia | Hoto: saharareporters.com
Asali: UGC

‘Yan ta'addan, sanye da bakaken kaya, sun yi tattaki a manyan tituna da kasuwanni inda suka tilasta wa ‘yan kasuwa da mazauna yankin bin umarnin zama a gida na kwanaki biyu a ranakun Alhamis 5 ga Mayu da Juma’a 6 ga Mayu.

An ce sun gargadi mazauna garin kan illar rashin bin umarnin zaman gidan da ake sa ran za a yi a fadin jihohin Kudu maso Gabas domin nuna adawa da ziyarar da shugaban kasa Muhammadu Buhari a jihar Ebonyi, kamar yadda SaharaReporters ta ruwaito.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Wata majiya ta ce lamarin ya faru ne a yayin da ‘yan ta'addan ke ci gaba da yada bayanansu wanda aka ce ya sanya wasu masu shaguna rufe rumfunansu.

A yayin da suka isa mahadar Uratta, sun yi artabu da sojoji wanda ya kai ga harbe-harbe, inda suka kashe hudu daga cikin ‘yan ta'addan, ciki har da shugabansu, yayin da wasu suka tsere da raunukan harbin bindiga.

Kara karanta wannan

Rokon da Shugaba Buhari ya yi, ya fada a kan kunnen kashi, ASUU ta cigaba da yajin-aiki

Wata majiyar soji a birgediya ta 14 da ta nemi a sakaya sunanta ta tabbatar da arangamar da ta kai ga mutuwar hudu daga cikin ‘yan bindigar, yayin da wasu suka samu raunuka.

Hakazalika majiyar ta tabbatar da kwato layu da kunkuru daga hannun wanda ake zargin shugaban tawagar ne.

Buhari ya yi Allah-wadai da fille kan ma'auratan sojoji biyu, ya dauki mataki

A wani labarin, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya umurci hukumomin soji da sauran jami’an tsaro da su yi iyakacin kokarinsu wajen kamo wadanda suka fille kan wasu sojoji biyu ma'aurata tare da gurfanar da su gaban kotu.

Shugaban kasar, a wata sanarwa da ya fitar a ranar Laraba ta hannun mai taimaka masa kan harkokin yada labarai, Garba Shehu, ya yi Allah wadai da fille kan jami'an da kungiyar ‘yan ta’adda ta IPOB, ta yi a ranar Asabar, kamar yadda rundunar sojin Najeriya ta tabbatar.

Kara karanta wannan

'Yan Bindiga Sun Kashe Sojoji 6 Yayin Da Suka Kai Wa Tawagar Kwamanda Hari a Taraba

Rahotanni sun bayyana yadda wasu sojoji biyu, Audu Linus da Gloria Matthew, suka mutu sakamakon fille kawunansu da aka yi a lokacin da suke kan hanyar zuwa jihar Imo domin bikin aurensu na gargajiya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel