'Yan Bindiga Sun Kashe Sojoji 6 Yayin Da Suka Kai Wa Tawagar Kwamanda Hari a Taraba

'Yan Bindiga Sun Kashe Sojoji 6 Yayin Da Suka Kai Wa Tawagar Kwamanda Hari a Taraba

  • Wasu miyagun yan bindiga sun afka wa tawagar sojoji a Taraba sun halaka sojoji shida da kwamandansu
  • Lamarin ya faru ne a Tati da ke karamar hukumar Takum a yayin da sojojin suke hanyarsu na zuwa wani aiki misalin karfe 10 na safe
  • Wata takardan gidan soji da Premium Times ta gani ya ce yan bindigan sun fi sojojin yawa ne sosai kuma ba a tabbatar da adadin wadanda aka kashe ba a bangaren yan bindigan

Yan bindiga sun kashe sojoji shida yayin da suke hanyar su ta zuwa wurin da aka kai hari a Tati, wani ƙauye da ke karamar hukumar Takum, a cewar rundunar Sojojin Najeriya cikin wani sako na cikin gida da Premium Times ta gani.

A cewar takardar da rundunar sojojin ta bataliya 93 da ke Takum ta aike, kawo yanzu ba a gano inda kwamandan bataliyar, E.S. Okore, mai muƙamin laftanar kanal ya ke ba.

Kara karanta wannan

Ta'addanci: 'Yan ta'adda sun bindige jami'an 'yan sanda har 3 a jihar Neja

'Yan Bindiga Sun Kashe Janar Ɗin Soja Da Sojoji 6 a Taraba
Yan Bindiga Sun Kashe Sojoji 6 Yayin Da Suka Afka Wa Tawagar Kwamandan Sojoji. Hoto: The Nation.
Asali: UGC

Jaridar Premium Times ta rahoto cewa takardar ta ce lamarin ya faru ne misalin ƙarfe 10 na safiyar ranar 10 ga watan Mayu. Ta ce yan bindigan sun fi sojojin yawa sosai.

Takardar ta kuma ce ba za a iya tabbatar da adadin wadanda suka mutu a bangaren yan bindigan ba.

Sojoji sun ragargaji wasu yan bindiga a Tonga, sun kashe biyu sun kwato makamai

Ta kuma ce dakarun sojoji a Donga yayin da suke kauyen Anamun sun kashe yan bindiga biyu yayin da sauran suka tsere da rauni.

Ta ce an kwato AK 47 1, harsashin AK 47 biyu masu tsawon 7.62mn, pistol 1, harsashi masu tsawon 9mm 7, bindiga kirar gargajiya, layyu da kudi N15,120 a hannun yan bindigan bayan artabun.

Kara karanta wannan

Hoton Kwamandan Sojin da yan bindiga suka sace a Taraba ya bayyana

Kuma, sojoji da ke dawowa daga wani aikin kai taimako sun gamu da yan bindiga amma sun yi artabu da su sun fita.

Takardar ta ce har yanzu sojojin na aikin bincike da ceto a yankin.

Taraba a Arewa maso gabas na samun karuwar laifuka da garkuwa da mutane musamman a Jalingo, babban birnin Jihar.

'Yan Ta'addan Da Suka Kai Hari Sansanin Sojoji Na Kaduna Sun Ɗanɗana Kuɗarsu, Lai Mohammed

A bangare gudan, Gwamnatin Tarayya, a ranar Laraba ta ce yan ta'addan da suka kai hari sansanin sojoji da ke Birnin Gwari a Kaduna sun sha azaba a hannun sojoji a yayin da suka fatattake su, rahoton Daily Trust.

Ministan Labarai da Al'adu, Alhaji Lai Mohammed, ne ya bayyana hakan yayin da ya ke amsa tambayoyi kan tsaro bayan taron FEC da Shugaba Muhammadu Buhari ya jagoranta a Aso Villa a Abuja.

Kara karanta wannan

An kuma, Bam ya tashi a kusa da sansanin Sojojin Najeriya a babban birnin jihar Arewa

Rahotanni sun bayyana cewa sojoji 11 ne suka riga mu gidan gaskiya yayin da wasu da dama suka jikkata yayin harin na ranar Talata.

Asali: Legit.ng

Online view pixel