Kebbi 2023: Ban raba motoci ga wakilan APC ba, minista Malami ya magantu

Kebbi 2023: Ban raba motoci ga wakilan APC ba, minista Malami ya magantu

  • AGF Abubakar Malami ya musanta sayen motoci masu tsada ga wakilan jam’iyyar APC a jihar Kebbi gabanin zaben fidda gwani na gwamnonin jam’iyyar
  • Akwai zargin cewa ministan shari’a ya siya wa wakilan jam’iyyar APC motoci a wani yunkuri na ganin ya samu tikitin takarar gwamnan jihar Kebbi daga jam’iyyar
  • Da yake musanta zargin, Malami ya ce abokansa da mukarrabansa ne suka bayar da gudumawa tare da raba motoci ga ma’aikatan gidauniyar Khadimiyya

Birnin Kebbi, jihar Kebbi – Abubakar Malami, Babban Lauyan Gwamnatin Tarayya (AGF) kuma Ministan Shari’a, ya yi magana kan wasu motoci masu tsada da aka baiwa wasu mukarrabansa a Kebbi.

Hotunan motoci masu tsada da ake zargin an baiwa wasu ma'aikatan gidauniyar Khadimiyya da ministan ya kafa sun yadu a shafukan sada zumunta.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Ministan Buhari Da Ya Yi Murabus Don Takarar Gwamna Ya Janye Takararsa

Batun raba motoci da ministan Buhari ya yi
Kebbi 2023: Ban raba motoci ga wakilan APC, inji ministan shari'a Malami | Hoto: @KBStGovt, @daily_trust
Asali: Twitter

Kyaututtukan dai sun haifar da martani daban-daban inda wasu ke ikirarin cewa Malami ya bayar da motocin ne a wani yunkuri na neman tikitin takarar gwamna na jam’iyyar APC a Kebbi a zaben 2023.

Sai dai kakakin AGF, Umar Gwandu ya musanta zargin tare da yin karin bayani.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Malami ya musanta raba motoci

A wata tattaunawa da manema labarai a Birnin Kebbi, babban birnin jihar Kebbi, a ranar Talata, 3 ga watan Mayu, Malami da kan sa ya yi watsi da wannan jita-jita, inji rahoton Daily Trust.

Yace:

“A halin yanzu, na fuskanci hare-hare da dama, hagu, dama da tsakiya, wasu na cikin gida wasu kuma na kasa da kasa, harin da ke da alaka da zargin cewa na raba motoci masu tsada da yawa ga wakilan jam’iyyar APC.
"A matsayina da wasu abokan hulda ta, ni ko wani abokina ba mu raba wata mota ga kowane wakili a fadin jihar ba."

Kara karanta wannan

Rokon da Shugaba Buhari ya yi, ya fada a kan kunnen kashi, ASUU ta cigaba da yajin-aiki

Malami ya bayyana labarin a matsayin batanci da rashin fahimta.

Gaskiyar me ya faru, Malami ya yi bayani

A bangare guda, AGF ya bayyana cewa abokansa da mukarrabansa ne suka bayar da gudummawar motoci ga ma’aikatan da suka dade suna aiki a gidauniyar Khadimiyya, in ji rahoton PM News.

A kalamansa:

“Bari in bayyana karara cewa wasu daga cikin gidauniyoyi, na Khadi Malami da gidauniyar samar da adalci da ci gaba ta Khadimiyya na kasance tare dasu na tsawon lokaci, suna da ma’aikata da suka nuna kwazo wajen ci gaban jihar.
“Wadannan kungiyoyi sun bayar da gudunmawa sosai wajen rage radadin talauci, samar da ababen more rayuwa ga lungu da sako, da karfafa matasa da mata marasa aikin yi, da kanana da matsakaitan manoma da ‘yan kasuwa da mata da sauran su a jihar.
“Saboda yaba aikin da ma’aikatan kungiyar ke yi a jihar da kuma wajenta, magoya bayan kungiyoyin a dunkule da kuma daidaiku suka yanke shawarar neman tallafi daga ’yan Najeriya masu kishin kasa da suke tallafa wa kungiyoyi masu zaman kansu domin ba da lada ga wadanda suke rike da ragamar kungiyoyin."

Kara karanta wannan

Sanatan Kebbi ta tsakiya: Alaka ta yi tsami tsakanin Aliero da Gwamna Bagudu kan wanda zai mallaki tikitin APC

Ban ba wakilan APC kyautar motoci ba, inji Malami

AGF Malami ya ce ko da yake ya tattauna da masu ruwa da tsaki na jam’iyyar APC kwanakin baya kuma ya karbi kiraye-kirayen da mutanen Kebbi suka yi masa na ya tsaya takarar gwamnan jihar; taron dai ba na rabon motoci ne ga masu ruwa da tsaki na jam’iyyar APC ba.

A cewarsa:

“Babu daya daga cikin masu ruwa da tsaki na jam’iyyar APC ko wakili a jihar Kebbi da na ba wa wata mota, kuma har yanzu ban ba wa kowa abin hawa ba.
“Masu yada barna za su iya tuntubar Sakatariyar jam’iyyar APC ta kasa, su samu jerin sunayen masu ruwa da tsaki na jam’iyyar APC da wakilai a jihar Kebbi."

Malami ya sake nanata cewa "babu alaka tsakanin sunayen masu ruwa da tsaki na jam'iyyar APC da wadanda suka ci gajiyar motocin kuma ba su ma da wata alaka."

Kara karanta wannan

Gwamnan Kano, Abdullahi Ganduje, ya karbi Fom din takara kujerar Sanata

Ana binciken Hadiman Abubakar Malami kan ‘karbar kudi’ domin yi wa barayi afuwa

A wani labarin, hukumar EFCC ta tsare wasu daga cikin manyan jami’an ma’aikatar shari’a, ta yi masu tambayoyi a game da batun mutanen da aka yi wa afuwa.

Jaridar The Cable ta fitar da rahoto na musamman da ya bayyana cewa ana zargin ma’aikatan da rashin gaskiya wajen tattara wadanda aka yafewa laifinsu.

Wata majiya ta shaida cewa Hadiman Ministan shari’a, Abubakar Malami da ke da alhakin tattara sunayen mutanen da za ayi wa afuwa, sun shiga hannun EFCC.

Asali: Legit.ng

Online view pixel