Wata Sabuwa: Za a Maka Shugaba Buhari a Kotu Kan Tsawaita Wa'adin Mulkin Shugaban NIS

Wata Sabuwa: Za a Maka Shugaba Buhari a Kotu Kan Tsawaita Wa'adin Mulkin Shugaban NIS

  • Wani mai rajin kare hakkin bil’adama, Inibehe Effiong, ya yi barazanar yin karar Gwamnatin Tarayya akan yadda Shugaban kasa ya dauki wani matakin tsawaita wa'adin shugaban NIS
  • Rahotanni sun nuna, sun Shugaba Buhari ya tsawaita wa’adin mataimakin shugaban hukumar kula da Shige da Fice ta Kasa, Isah Jere wanda yanzu shi ne mukaddashin shugaban hukumar
  • Effiong ya yi mamakin yadda shugaban kasa ya kasa zaben wani shugaban hukumar duk da yadda akwai jami’ai da dama da suka cancanci dare wa kujerar

Inibehe Effiong, wani mai rajin kare hakkin bil’adama, ya na barazanar maka gwamnatin tarayya kara akan yadda Shugaba Muhammadu Buhari ya tsawaita wa’adin Shugaban Hukumar Kula da Shiga da Fice ta Kasa, NIS, Isah Jere wanda shi ne yanzu haka mukaddashin shugaban hukumar.

A cewar Effiong, hakan bai dace ba kuma mummunan abu ne ace Shugaban kasa yana wofantar da ayyukan al’umma, The Punch ta rahoto.

Kara karanta wannan

'Batanci: Bayan Buhari Ya Yi Allah Wadai Da Kisan Deborah a Sokoto, Osinbajo Ya Yi Magana Da Kakkausar Murya

Za a Maka Buhari a Kotu Kan Tsawaita Wa'adin Mulkin Shugaban NIS
Mai rajin kare hakkin bil’adama na barazanar kai karar Buhari akan kara wa’adin shugaban Hukumar kula da Shiga da Fice ta Kasa. Hoto: The Punch.
Asali: Twitter

Ya yi mamakin dalilin da ya hana shugaban kasa zaben wani jami’in da ya cancanci hawa kujerar duk da kasancewar akwai manyan jami’an da su ka dace ya zaba.

An yi wa jami’ai jarabawa kuma 3 sun cancanci hawa kujerar

Naija Dailies ta ruwaito cewa Ma’aikatar Gwamnatin Tarayya ta harkokin cikin gida ta gwada jami’ai da dama kuma ta tattauna da su har ta zabi mutane 3 da suka fi cancanta.

An kai wa Buhari takardar ta ranar 15 ga watan Maris din 2022, don ya sa hannu akan ta. Jere, ba ya cikin wadanda su ka cancanci hawa kujerar don a ranar 24 ga watan Afirilu ya cika shekaru 60.

Amma an samu bayani akan yadda wasu mutane su ka ziyarci fadar shugaban kasa don su nemi alfarmar a kara wa Jere shekara daya akan kujerar.

Kara karanta wannan

Kungiyar Izalah tayi Allah wadai da zagin Annabi (SAW) da wata yarinya tayi a jihar Sokoto

Don haka Jere zai sauka daga kujerar ne ana saura wata daya wa’adin mulkin Buhari ya cika.

An siyasantar da nadin ne

Wata majiya ta bayyana cewa:

“Akwai manyan jami’an da su ka wuce jarabawar kuma an tattauna da su sannan ministan harkokin cikin gida, Rauf Aregbesola ya mika sunayensu ga shugaban kasa.
“Jere ba ya cikinsu. Amma an roki shugaban kasa ta hanyar wasu manyan na kusa da shi wadanda su ka ja hankalin shugaban ya kara masa wa’adi a kujerar.”

Ganin hakan ne Effiong ya ce za su maka Buhari a kotu akan tozarta dokar mukaman gwamnati.

A cewarsa:

“Ana bai wa mukaddashi damar ci gaba da zama a kujera ne idan ya cancanci hakan. Don haka idan bai cancanta ba, ba ya da damar rike kujerar.
“Ba doka bane kara masa wa’adin da shugaban kasa ya yi. Wannan yana nuna irin rashawar da gwamnatin Buhari ta ke yi saboda ba wannan ba ne karon farko da aka karya irin wannan dokar ba.

Kara karanta wannan

Sokoto: Tambuwal ya umarci a yi bincike kan kashe dalibar kwalejin da ta zagi Annabi

“Babu wani muhimmanci da karin wa’adin zai yi wa kasa amma kuma aka zabi ci gaba da barinsa akan kujerar.”

Shugaban kasa ya na da damar nada wanda ya so

Yayin da aka nemi jin ta bakin hadimin shugaban kasa na musamman a harkokin yada labarai, Garba Shehu, ya tabbatar da karin wa’adin Jere.

Mai ba Ministan harkokin cikin gida shawarwari akan harkar labarai, Sola Fasure ya ce karin wa’adin na siyasa ne. Inda ya kara da cewa shugaban kasa ya na da damar kara wa duk wanda ya so wa’adi.

Kamar yadda ya ce:

“Shugaban kasa ya na da damar nada duk wasu masu mukamai. Akwai matsayin da idan ka kai za ka iya nada wanda ka so. Shugaban kasa yana da damar nada wanda ya so a ko wacce ma’aikata.”

Asali: Legit.ng

Online view pixel