Kungiyar Izalah tayi Allah wadai da zagin Annabi (SAW) da wata yarinya tayi a jihar Sokoto

Kungiyar Izalah tayi Allah wadai da zagin Annabi (SAW) da wata yarinya tayi a jihar Sokoto

  • Shugaban kungiyar Izalah a Najeriya ta ya yi Allah wadai da abinda ya faru a jihar Sokoto
  • Bala Lau yace hukuma ce ke da hurumin yanke hukunci ga wanda ya zagi Annabi, ba ‘dai’daikun mutane ba
  • Ya kuma yi kira ga Hukumomi da su dinga zartar da hukuncin kisa ga wanda ya zagi Annabi (S) kafin jama’a su kai ga nasu hukuncin, Wannan ne kadai zai hana’dai’daikun mutane daukar mataki na kisa

Kungiyar wa’azin musulunci ta Izalatil Bidi’ah wa iqamatis sunnah a tarayyar Naijeriya tayi Allah wadai da wata yarinya wacce ba musulma ba da ta zagi Annabi Muhammadu tsira da aminci su kara tabbata a gare shi .

A jawabin da kungiyar ta saki, ta ce yarinyar ta kunduma ashariya ga Annabi (SAW) wanda duk musulmi bazaiji dadi ba, wanda hakan har yakai ga wasu jama’a suka kasheta kuma suka kona ta.

Kara karanta wannan

Batanci Ga Annabin Rahma (SAW), Dr Sani Umar Rijiyar Lemo

Tace:

"Addinin musulunci bai bada dama ga musulmi ya zagi ko wane Annabi daga Annabawan Allah ba, dan haka akwai bukatar shugabannin kiristoci su dauki aniyar wayar da kan mabiyansu akan illar taba mutunci ko zagin fiyayyen halitta wanda hakan ka iya tayar da husuma a cikin kasa."

Bala Lau
Kungiyar Izalah tayi Allah wadai da zagin Annabi (SAW) da wata yarinya tayi a jihar Sokoto Hoto: Jibwis Nigeria
Asali: Original

Shugaban Izalah, Sheikh Bala Lau, yayi kira na musamman ga hukuma da ta dinga saurin daukan mataki na kisa ga wanda ya zagi Annabi (S) da wannan shi zai hana jama’a daukar nasu matakin, amma jama’a suna ganin ko an damka wanda yayi zagin ga hukuma Masu kare hakkin dan Adam zasu shigo ayi ta bugawa wanda hakan zai sa a saki wanda yayi zagin, yaci gaba da rayuwar sa ba tare da daukan matakin na shari’a a kansa ba. “

Kara karanta wannan

'Batanci: Atiku Ya Ce Ba Shine Ya Wallafa Rubutun Sukar Kashe Ɗalibar Sokoto a Shafinsa Ba

Dan haka Ina kira ga hukumomi da su dinga aiwatar da hukuncin kisa ga wanda yayi zagin, Wannan ne kadai zai gamsar da mutane su daina daukar doka a hannunsu” Inji Shi.

Shugaban IZALA Sheikh Bala Lau ya kuma yi kira ga jama’a a duk lokacin da irin haka ya faru idan an kama wanda yayi zagin babu wani wanda yake da hakkin zartar wa wani haddi ko hukunci akan tuhumar da ake masa, har sai an gabatar da shi gaban alkali, shi ne wanda zai iya tabbatar masa da wannan laifin ko ya wanke shi.

Don haka dole ne jama’a su fahimci, kuma su fahimtar da cewa, wannan aiki da wasu suka dauka ba koyarwar musulunci ba ne, kuma ba wani malami na musulunci da ya taba fatawar aikata irin wannan aika-aika da sunan son Annabi (S.A.W), ko kishin musulunci, kuma musulunci yana tir da irin wannan ta’asa a duk inda aka yi ta.

A karshe shehin Malamin yayi kira ga hukumomi da kan daukan mataki domin hukunta masu irin wannan laifi da gaggawa don toshe kafar hana irin wannan saboda masu daukan doka a hannu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel