Iftila'i: Fasinjoji 50 sun tsallake rijiya da baya yayin da tayar jirgi ta kama da wuta

Iftila'i: Fasinjoji 50 sun tsallake rijiya da baya yayin da tayar jirgi ta kama da wuta

  • An ceto fasinjoji 50 a lokacin da tayar da jirgin saman Dana Air ta kama a filin tashi da saukar jiragen sama na Fatakwal
  • An dakatar da tashin jirgin #9J344 a Fatakwal zuwa Legas saboda abin da matukin jirgin ya ce an samu matsala a cikin jirgin
  • Sakamakon hayakin birki da ya wuce kima, gobara ta tashi daga tayar jirgin, amma an kasheta a lokacin da jirgin ke isa kan titin tashi

Omagwa – An samu tangardar tashin jirgi a filin jirgin sama na Fatakwal, Omagwa lokacin da tayar jirgin Dana Air da ya nufi Legas ta kama wuta.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa an kwashe fasinjoji 50 da ke cikin jirgin nan take yayin da matukin jirgin ya gimtse tashin.

Sai an taki babban sa'a, domin kuwa an sauke dukkan mutanen da ke cikin jirgin lafiya.

Kara karanta wannan

Nisan kwana: Yadda fasinjan da bai iya tuki ba ya ceto jirgin da direbansa ya rikice a sama

Jirgin sama ya kusan samun matsala a Fatawal
Iftila'i: Fasinjoji 50 sun tsallake rijiya da baya yayin tayar jirgi ta kama da wuta | Hoto: @DanaAir
Asali: Twitter

Dana Air ya mayar da martani, ya ce amincin fasinja shi ne gaba kan komai

Wata sanarwa da mai magana da yawun Dana Air, Kingsley Ezenwa ya wallafa a shafin Twitter ta tabbatar da faruwar lamarin.

Wani bangare na sanarwar ya karanta:

“Jirgin mu mai rajista 5N JOY mai lamba 9J 344 daga Fatakwal zuwa Legas a ranar 2 ga watan Mayun 2022, ya shirya tashi sai direban jirgin ya lura da wata matsala da ya nemi taimakon hukumar kula da zirga-zirgar jiragen sama kafin ya hau kan hanya daidai da tsauraran matakan aikin mu na aminci.
“Duk da haka, tasirin birki a sakamakon tsayuwar jirgin ya yi ya shafi tayoyin jirgin da suka kama da wuta a lokacin da jirgin ke kokarin tsayawa.

Kara karanta wannan

Da Duminsa: Ɗiyar tsohon ministan Abuja da wasu mutum 11 sun mutu a hatsarin jirgin sama

“Dukkan fasinjoji 50 da ke cikin jirgin sun sauka lafiya, kuma nan take tawagarmu ta kula da jirgin ta dakatar da jirgin har sai an kammala bincike.
"Haka kuma, muna ba da hakuri ga dukkan fasinjojin da ke cikin jirgin saboda matsalar da hakan ya haifar sakamakon soke tashin jirgin."

Haruna Elijah Karatu: Hotunan matukin jirgi NAF na 2 da ya rasa ransa a hatsarin Kaduna

A wani labarin, an gano waye dayan matukin jirgin NAF da ya rasa ransa a hatsarin jirgin dakarun da ya auku a ranar Talata a Kaduna. Hafsan sojan mai suna Lieutenant Haruna Elijah Karatu, ya rasu ne sanadiyyar hatsarin da jirginsu ya tafka a jiya Talata.

Vanguard ta ruwaito cewa, Karatu ya rasa ransa ne yayin hatsarin tare da abokin aikinsa, Abubakar Alkali, 'dan jihar Yobe.

An samu labarin yadda Karatu ya yi kwalejin Gwamnatin Tarayya ta Sakkwoto da Kwalejin Christ Ambassadors, kafin ya shiga makarantar horar da hafsun sojin Najeriya ta jihar Kaduna.

Kara karanta wannan

Karin Bayani: Wani Jirgin sama ɗauke da Fasinjoji 11 ya yi hatsari a cikin Daji

Asali: Legit.ng

Online view pixel