Yar Najeriya mai tuƙa jirgin sama da wasu mutum 11 sun mutu a sabon haɗarin Jirgi

Yar Najeriya mai tuƙa jirgin sama da wasu mutum 11 sun mutu a sabon haɗarin Jirgi

  • Ɗiyar tsohon ministan Abuja kuma jigo a PDP, Solomon Ewuga, da ke aikin tuƙin jirgin sama ta mutu tare da wasu mutum 11 a haɗarin jirgi
  • Bayanai sun nuna cewa Adzuayi Ewuga, ta rasa rayuwarta ne bayan karamin jirgin ya rasa sadarwa da Filin jirgi
  • Jirgin ya yi hatsari ne a kudancin babban birnin ƙasar Kamaru bayan ya taso daga filin sauka da tashin jirage na Yaounde Nsimalen

Matuƙiyar jirgin sama yar Najeriya, Adzuayi Ewuga, ta rasa rayuwarta a wani hatsarin jirgin sama da ya rutsa da ita a tsakiyar ƙasar Kamaru, kamar yadda Leadership ta ruwaito.

Marigayyar ɗiya ce ga Sanata Solomon Ewuga, wani jigo a jam'iyyar hamayya PDP a jihar Nasarawa kuma tsohon ƙaramin ministan babban birnin tarayya, Abuja.

Kara karanta wannan

Dalibai mata na jami'o'i biyu a Arewa zasu fito tituna zanga-zanga tsirara kan yajin aikin ASUU

Adzuayi Ewuga ta mutu a haɗarin jirgi.
Yar Najeriya mai tuƙa jirgin sama da wasu mutum 11 sun mutu a sabon haɗarin Jirgi Hoto: leadership.ng
Asali: UGC

Matuƙiyar jirgin ta mutu ne tare da wasu mutum 11 a wani ƙaramin jirgi mallakin Ma'aikatar kula da harkokin sufurin jiragen sama na Kamaru, wanda ya yi hatsari sanadiyyar katsewar sadarwa.

Rahotanni sun bayyana cewa jirgin ya taso ne daga filin jirgin Yaounde Nsimalen ya nufi Belabo da ke gabashin ƙasar ƙasar, lokacin da haɗarin ya auku, duk na ciki suka mutu.

Ma'aikatar kula da harkokin sufurin jirgi ta Kamaru na da alaƙa da Caverton Offshore Support Group, da ke Legas a Najeriya, kuma sukan taimaka wa jiragen Kamaru, kamar yadda Vanguard ta ruwaito.

Legit.ng ta tattaro cewa wannan shi ne babban haɗarin jirgi na farko da ya auku a Kamaru tun bayan abin da ya farua shekarar 2007.

A wani labarin na daban kuma Sheikh Ɗahiru Usman Bauchi ya bayyana sunan ɗan takarar da yake rokon Allah ya gaji Buhari a 2023

Kara karanta wannan

Cikakken Labari: Wani Bam Ya Tashi a Masallaci Yayin da Mutane ke tsaka da Sallar Jumu'a

Fitaccen Malamin addinin Musulunci a Najeriya, Sheikh Ɗahiru Bauchi, ya nuna goyon bayansa ga Yemi Osinbajo a zaɓen 2023.

Malamin ya ce ya jima ya na wa mataimakin shugaban Addu'a don haka zai nunka rokon Allah ya samu nasara a zaɓe.

Asali: Legit.ng

Online view pixel