Haruna Elijah Karatu: Hotunan matukin jirgi NAF na 2 da ya rasa ransa a hatsarin Kaduna

Haruna Elijah Karatu: Hotunan matukin jirgi NAF na 2 da ya rasa ransa a hatsarin Kaduna

  • An gano gawar dayan matukin jirgin NAF, mai suna Lieutenant Haruna Elijah Karatu, wanda ya rasa ransa a hatsarin jirgin NAF a Kaduna
  • Karatu, wanda shine matukin jirgin NAF da ya yi hatsari ya rasa ransa ne tare da abokin aikinsa, Abubakar Alkali daga jihar Yobe
  • Kafin mutuwar matukan jirgin, jami'an sojin na daga cikin wadanda suka dawo daga Pakistan a Afirilun 2021 bayan samun horarwa a nahiyar Asiya

An gano waye dayan matukin jirgin NAF da ya rasa ransa a hatsarin jirgin dakarun da ya auku a ranar Talata a Kaduna. Hafsan sojan mai suna Lieutenant Haruna Elijah Karatu, ya rasu ne sanadiyyar hatsarin da jirginsu ya tafka a jiya Talata.

Vanguard ta ruwaito cewa, Karatu ya rasa ransa ne yayin hatsarin tare da abokin aikinsa, Abubakar Alkali, 'dan jihar Yobe.

Kara karanta wannan

Bidiyon yadda fasinja ta yanke jiki ta fadi, tace ga garinku a filin jirgin sama dake Abuja

An samu labarin yadda Karatu ya yi kwalejin Gwamnatin Tarayya ta Sakkwoto da Kwalejin Christ Ambassadors, kafin ya shiga makarantar horar da hafsun sojin Najeriya ta jihar Kaduna.

Haka zalika, jami'an sojin guda biyu su na daga cikin jami'an da suka dawo daga Pakistan a watan Afirilu, 2021 bayan samun horarwa na tsawon watanni shida a nahiyar Asiya, Daily Trust ta ruwaito.

Haruna Elijah Karatu: Hotunan matukin jirgi NAF na 2 da ya rasa ransa a hatsarin Kaduna
Haruna Elijah Karatu: Hotunan matukin jirgi NAF na 2 da ya rasa ransa a hatsarin Kaduna. Hoto daga dailytrust.com
Asali: UGC

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Haruna Elijah Karatu: Hotunan matukin jirgi NAF na 2 da ya rasa ransa a hatsarin Kaduna
Haruna Elijah Karatu: Hotunan matukin jirgi NAF na 2 da ya rasa ransa a hatsarin Kaduna. Hoto dailytrust.com
Asali: UGC

Haruna Elijah Karatu: Hotunan matukin jirgi NAF na 2 da ya rasa ransa a hatsarin Kaduna
Haruna Elijah Karatu: Hotunan matukin jirgi NAF na 2 da ya rasa ransa a hatsarin Kaduna. Hoto daga dailytrust.com
Asali: UGC

Jirgin saman sojoji ya hatsari a Kaduna, jami'ai 2 sun mutu

A wani labari na daban, a yammacin ranar Talata ne wani jirgin horar da sojojin saman Najeriya ya yi hatsari a garin Kaduna, Arewa maso Yammacin Najeriya.

Majiyoyi sun ce ana fargabar mutuwar matukan jirgin biyu da ke cikinsa yayin hatsarin, inji rahoton Leadership.

Wata majiya ta shaida cewa, jirgin na Super Mushak na horar da jami'ai ya yi hatsari ne a cibiyar NAF ta Kaduna a lokacin da ya ke aikin horor da jami'an tsaron.

Kara karanta wannan

Jerin haɗurran Jiragen Sojojin Najeriya da suka lakume rayukan manyan Jami'ai a shekara ɗaya

Asali: Legit.ng

Online view pixel