Da Dumi-Dumi: Jirgin sama makare da mutane ya yi haɗari a Kamaru

Da Dumi-Dumi: Jirgin sama makare da mutane ya yi haɗari a Kamaru

  • Wani ƙaramin jirgin saman fasinja ya yi hatsari a wani daji da ke kudancin babbar birnin ƙasar Kamaru, Yaounde
  • Ma'aikatar kula da sufuri ta ƙasar ta sanar da cewa jirgin mai ɗauke da Fasinja 11 ya yi haɗarin ne ranar Laraba
  • Rahoto ya nuna cewa har yanzun ba'a gano musabbabin faɗuwar jirgin ba, amma ana gani sadarwa ce ta katse wa matuƙin

Cameroon - Wani jirgin sama mai ɗaukar Fasinjoji ya yi haɗari a kusa da babban birnin kasar Kamaru, Yaounde ranar Laraba, kamar yadda BBC Hausa ta ruwaito.

Da take tabbatar da faruwar lamarin, ma'aikatar kula da harkokin sufuri ta kasar, ta bayyana cewa karamin jirgin saman dake ɗauke da mutane 11 ya yi hatsari ne a wani daji dake Kudu da Yaounde.

Jirgim sama yana tsaka da tafiya.
Da Dumi-Dumi: Jirgin sama makare da mutane ya yi haɗari a Kamaru Hoto: usatoday.com
Asali: UGC

Rahotanni sun nuna cewa har yanzun ba'a gano musabbabin da ya yi sanadin hatsarin ba, amma wasu bayanai sun bayyana cewa sadarwa ce da datse tsakanin matukin da kuma filin jirgi.

Kara karanta wannan

Cikakken Labari: Wani Bam Ya Tashi a Masallaci Yayin da Mutane ke tsaka da Sallar Jumu'a

Bayan jirgin ya ɓata yayin da sadarwa ta katse, aka zurfafa bincike daga bisani aka gano shi a wani jeji da ke kusa da Nanga Eboko, wurin na da nisan kilomita 150 daga birnin Yaounde.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ina jirgin ya nufa kafin haɗarin?

A cewar ma'aikatar kula da harkokin sufurin, jirgin ya taso ne daga filin sauka da tashin jirgen saman Nsimalen kuma ya nufi garin Belabo ne da ke gabashin ƙasar ta Kamaru.

A rahoton da kamfanin dillancin labarai na APF ya ruwaito, ya nuna cewa wani Kamfanin Mai me zaman kansa da ake kira CETCO a takaice, shi ne ya ɗauki shatar jirgin.

Bayanai sun ce tun bayan abun da ya faru a shekarar 2007, wannan ne karo na farko da aka samu babban hatsarin jirgin sama a Kamaru.

Legit.ng Hausa ta tattaro cewa a wancan lokacin wani Jirgin saman ƙasar Kenya ɗauke da mutane sama da 100 ya yi hatsari jim kaɗan bayan tashinsa daga birnin Douala

Kara karanta wannan

Nisan kwana: Yadda fasinjan da bai iya tuki ba ya ceto jirgin da direbansa ya rikice a sama

A wani labarin na daban kuma Sheikh Ɗahiru Usman Bauchi ya bayyana sunan ɗan takarar da yake rokon Allah ya gaji Buhari a 2023

Fitaccen Malamin addinin Musulunci a Najeriya, Sheikh Ɗahiru Bauchi, ya nuna goyon bayansa ga Yemi Osinbajo a zaɓen 2023.

Malamin ya ce ya jima ya na wa mataimakin shugaban Addu'a don haka zai nunka rokon Allah ya samu nasara a zaɓe.

Asali: Legit.ng

Online view pixel