Kano: Ganduje ya haramta zuwa da fostoci masallatan idi ko wurin shagulgulan sallah

Kano: Ganduje ya haramta zuwa da fostoci masallatan idi ko wurin shagulgulan sallah

  • Gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje ya haramta yawo da manya da kananan fostocin kamfen a filin sallar Idi ko wajen shagalin bikin sallah
  • A ganinsa, hakan na dauke hankalin jama'a daga bauta, sannan yana haddasa rikici tsakanin jam'iyyun adawa, musamman a Hawan Daushe
  • Ya ja kunnen jama'a da kada su kuskura su yi yawon kamfen yayin da ake tsaka da shagalin bikin sallah, sannan ya bukaci 'yan jihar da su cigaba da yi wa jihar da kasa addua

Kano - Gwamna Abdullahi Umar Ganduje na jihar Kano ya haramta yawo da manyan fostoci da kanana yayin sallar Idi da sauran shagulgulan sallah, Daily Trust ta ruwaito.

A sakon sallanshi da kwamishinan yada labarai, Malam Muhammad Garba ya fitar a wata takarda, gwamnan ya ce hakan zai iya kawar da hankali daga sallah.

Kara karanta wannan

Sokoto: Tambuwal ya umarci a yi bincike kan kashe dalibar kwalejin da ta zagi Annabi

"Yayin da ake ganinsu bauta mai matukar muhimmanci bayan tsawon lokacin da aka dauka ana azumin Ramadana, inda shagulgulan al'adu ke biyo baya."
"Saboda haka, baya kyautuwa ga mutum ko jam'iyyar siyasa su rage wa wurin bautar kima ta hanyar amfani da kayayyakin kamfen," a cewarsa.

Ganduje ya ce, yawo da fostoci yayin da mutanen jam'iyyu daban-daban suke filin bauta ko shagulgulan sallah, musamman bikin shagalin al'ada na hawan daushe a fadar sarki, yana tada tarzomar siyasa.

Punch ta ruwaito cewa, ya ja kunnen jama'a da kada su karfafa kamfen na siyasa yayin bikin sallah.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Haka zalika, gwamnan ya shawarci 'yan siyasa dake jihar da su yi biyayya ga tsarin hukumar gudanar da zabe mai zaman kanta ta tsara na ayyukan zaben shekarar 2023.

Daga karshe, ya roki musulman fadin jihar da su cigaba da yi wa jihar addu'a da kasa baki daya.

Kara karanta wannan

Billahil lazi la ilaha illahuwa za mu rike maka amanarka – Gawuna ga Ganduje

Kano: An sako Muhuyi Rimin Gado daga gidan yari bayan cika sharuddan beli

A wani labari na daban, tsohon shugaban hukumar yaki da rashawa na jihar Kano (PCACC) da aka dakatar, Muhuyi Rimingado ya samu 'yanci bayan cika ka'idojin da aka gindaya masa kafin a sake shi.

Daily Nigerian ta tattaro yadda Rimingado ya sake ganawa da iyalinsa a gidansa dake titin Yahaya Gusau.

Wata kotun majistare dake Kano karkashin jagorancin babban alkali Aminu Gabari ta bada belin Rimingado a ranar Juma'a bayan gurfanar dashi da aka fara yi.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel