Da duminsa: 'Yan bindiga sun kai wa motar kudi farmaki a Imo

Da duminsa: 'Yan bindiga sun kai wa motar kudi farmaki a Imo

  • Miyagun 'yan bindiga a jihar Imo sun budewa motar banki wuta a kan hanyarta daga Mbaise zuwa Owerri a ranar Alhamis
  • Ganau sun sanar da yadda direban motar yasha da kyar bayan motar ta kwace masa ya dinga tintsirawa kan wasu ababen hawan
  • Sai dai jama'a sun sanar da yadda ababen hawa hudu suka lalace sakamakon barnar da motar bakin ta yi musu

Imo - 'Yan bindiga sun bude wuta kan wata motar banki dake tafiya daga Mbaise zuwa Owerri a ranar Alhamis a karamar hukumar Mbaise da ke jihar Imo.

Vanguard ta tattaro cewa, lamarin ya faru wurin karfe 2 na rana a Ogbor Nguru dake Nwankwo a karamar hukumar Mbaise a jihar.

Da duminsa: 'Yan bindiga sun kai wa motar kudi farmaki a Imo
Da duminsa: 'Yan bindiga sun kai wa motar kudi farmaki a Imo. Hoto daga Vanguardngr.com
Asali: UGC

The Cable ta ruwaito cewa, an gano cewa, 'yan bindigan na kyautata tsammanin cewa motar dankare take da kudi kuma za ta kai su inda ya dace ne amma sai suka same ta babu komai ciki.

Kara karanta wannan

Harin jirgin Abj-Kad: Daya daga cikin matan da aka sace ta haihu a hannun 'yan bindiga

Wani ganau ba jiyau ba ya sanar da yadda 'yan bindigan suka dinga harbi babu kakkautawa inda direban motar da wasu mutum biyu a kokarinsu na tserewa suka dinga tintsirawa.

Direban motar kudin ya tsere bayan motar ta dinga tintsirawa kuma ta fada kan wasu ababen hawa har hudu da ke ajiye a wurin. Ta ragargaza ababen hawan tare da lalata tagogi, kofofi da kuma gilasan ababen hawan.

Kamar yadda ganau din yace: "Motar kudi dauke da kudi daga Owerri zuwa Mbaise ta ci karo da farmakin 'yan bindiga a Ogbo Nuguru da ke karamar hukumar Aboh Mabise.

"Motar kudin ta tintsira tare da lalata wasu motoci har hudu da aka ajiye a yankin.

"Direban motar kudin ya sha da kyar amma motarsa ta lalata ababen hawan wasu a yankin. Wadannan ababen hawan duk sun tashi aiki amma muna Godiya ga Ubangiji da yasa direban ya samu kansa lafiya."

Kara karanta wannan

Na Ɗauka Barewa Ne: Mafarauci Ya Bindige Limamin Ƙauyensu Har Lahira a Osun

A lokacin rubuta wannan rahoton, jami'an tsaro sun riga sun hallara inda lamarin ya faru.

Sama da rayuka 100 sun salwanta sakamakon gobara da ta tashi a matatar man fetur din sata a Imo

A wani labari na daban, a kalla rayuka 100 ne suka salwanta sakamakon fashewar wani abu a matatar man fetur na sata dake Ohaji a karamar hukumar Egbema ta jihar Imo.

Lamarin, wanda ya fara wurin karfe 11 na daren Juma'a, ya yi sanadiyyar tashin gagarumar gobara a Ohaji da ke yankin Egbema, Thecable ta ruwaito.

A yayin jawabi kan lamarin, Gwamna Hope Uzodinma na jihar Imo, wanda ya samu wakilcin Goodluck Opiah, kwamishinan lamurran man fetur, ya ce matasa da yawa sun rasa rayukansu sakamakon gobarar, amma har yanzu ba a kididdige yawan wadanda suka rasa rayukansu ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel