Hoton Kwamandan Sojin da yan bindiga suka sace a Taraba ya bayyana

Hoton Kwamandan Sojin da yan bindiga suka sace a Taraba ya bayyana

  • An bayyana hoton jagoran Sojojin da yan bindiga suka kashe yaransa sannan suka yi awon gaba da shi
  • Yan bindiga sun hallaka kimanin Sojoji shida a harin kwantan baunan da suka kai makon nan
  • Hukumar Sojin Najeriya ta ce an kaddamar da yunkurin ceto jami'in Sojan dake hannun yan ta'addan

Taraba - Hoton Kwamandan Sojin Najeriya, Laftanan Kanal Ememike S. Okore (N/11717) da tsagerun yan bindiga masu garkuwa da mutane suka sace a jihar Taraba ya bayyana.

Sahara Reporters a rahoto tace an yi awon gaba da Ememike Okore ne sakamakon harin kwantan baunan da yan bindiga suka kaiwa Sojojin ranar Talata.

Yan bindigan sun kashe jami'an Sojoji shida yayinda suka yi awon gaba da kwamandansu.

Kara karanta wannan

Ta'addanci: 'Yan ta'adda sun bindige jami'an 'yan sanda har 3 a jihar Neja

Hoton Kwamandan Soji
Hoton Kwamandan Sojin da yan bindiga suka sace a Taraba ya bayyana Hoto: saharareporters.com
Asali: UGC

Kakakin hukumar Sojin Najeriya, Onyema Nwachukwu, a jawabin da ya fitar ranar Laraba ya bayana cewa rundunar 93 Bataliya sun shiga neman Sojan da aka sace don cetosa.

A cewarsa:

"Sojoji yanzu haka na bibiyan yan bindigan kuma ba zasu yi kasa a gwiwa ba wajen ceto jami'in da ya bace"
"Muna kira ga al'ummar jihar Taraba su kasance cikin farga kuma su bada rahoton duk wani bakon abu ga hukumomin tsaro."'

'Yan Bindiga Sun Kashe Sojoji 6

Mun kawo muku cewa yan bindiga sun kashe sojoji shida yayin da suke hanyar su ta zuwa wurin da aka kai hari a Tati, wani ƙauye da ke karamar hukumar Takum.

A cewar takardar da rundunar sojojin ta bataliya 93 da ke Takum ta aike, kawo yanzu ba a gano inda kwamandan bataliyar, E.S. Okore, mai muƙamin laftanar kanal ya ke ba.

Kara karanta wannan

An kama wani Soja da ke sayarwa yan bindiga makamai a Zamfara, ya yi bayani dalla-dalla

Jaridar Premium Times ta rahoto cewa takardar ta ce lamarin ya faru ne misalin ƙarfe 10 na safiyar ranar 10 ga watan Mayu. Ta ce yan bindigan sun fi sojojin yawa sosai.

Takardar ta kuma ce ba za a iya tabbatar da adadin wadanda suka mutu a bangaren yan bindigan ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel