Borno: 'Yan ta'addan Boko Haram sun kai hari ana tsaka da shagalin biki

Borno: 'Yan ta'addan Boko Haram sun kai hari ana tsaka da shagalin biki

  • 'Yan ta'addan Boko Haram sun kai mummuna hari wurin wani shagalin bikin aure tare da nadin sarauta a Kindila dake Askira Uba, jihar Borno
  • Sun bude wa mahalartan wurin wuta inda suka dinga harbe-harbe kafin su tafi da wani dan banga wanda suka sheke daga bisani
  • Mazauna yankin sun tabbatar da aukuwar lamarin inda suke bayyana yadda 'yan ta'addan yanzu suka addabi farar hula

Askira Uba, Borno - An rasa ran mutum daya inda wasu da dama suka jigata yayin da mayakan ta'addancin Boko Haram/ISWAP suka kai farmaki wurin wani shagalin aure a kauyen Kindila na karamar hukumar Askira Uba ta jihar Borno.

Kamar yadda wata majiya ta sanar, maharan sun bayyana a cikin manyan motoci biyu kuma suka tare hanyar fita yayin da suke ta harbe-harbe kan duk wanda suka samu, al'amarin da yasa mutane suka dinga gudu domin tseratar da rayukansu, Aminiya Daily Trust ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: Wani Bam ya ƙara fashewa a babban birnin jihar Arewa, ya shafi mutane da dama

Borno: 'Yan ta'addan Boko Haram sun kai hari ana tsaka da shagalin biki
Borno: 'Yan ta'addan Boko Haram sun kai hari ana tsaka da shagalin biki. Hoto daga thecable.ng
Asali: UGC
"Daga bisani miyagun sun halaka wani dan banga mai suna Suleiman sa'in da suka tafi da shi. An ga gawar marigayin," wata majiya ta tabbatar.

'Yan ta'addan sun kai harin cikin kauyen ana tsaka da bikin aure da na nadin sarauta inda suka bude wa mahalarta wuta, cewar wata majiya daga Zagazola Makama.

A cikin kwanakin nan, 'yan ta'addan sun tsananta kai wa fararen hula farmaki har da wuraren shakatawa a jihar ta Borno, abinda ke janyo rashin rayuka na fararen hula da basu ji ba, ba su gani ba.

'Yan ta'addan ISWAP sun yi ikirarin alhakin halaka 'yan sanda 3 a Kogi

A wani labari na daban, kungiyar ta'addanci ta ISWAP ta tabbatar da alhakin kaiwa wani ofishin 'yan sanda hari a jihar Kogi.

Kara karanta wannan

'Yan Bindiga Sun Kai Sabon Hari a Zamfara, Sun Harbi Mutane, Sun Sace Dabobi Masu Yawa

The Cable ta ruwaito yadda 'yan bindiga suka kai hari wani ofishin 'yan sanda a karamar hukumar Adavi a safiyar Asabar, gami da halaka 'yan sanda uku.

Edward Egbuka, kwamishinan 'yan sandan jihar, ya siffanta mummunan lamarin a matsayin "harin ba-zata."

Kamar yadda Voice of America ta bayyana, a wata takarda da ISWAP ta wallafa a Telegram, ta ce "Sojojin Halifan Musulunci sun kai wa ofishin 'yan sanda hari." Kungiyar ta kara da bayyana yadda aka halaka mutane biyar yayin kai harin.

Haka zalika, ISWAP ta bayyana yadda take da alhakin saka abu mai fashewa, wanda ya lashe rayukan mutane shida a kasuwa cikin Taraba a ranar Talata.

Asali: Legit.ng

Online view pixel