Sojoji 6 sun kwanta dama yayin da yan bindiga suka farmaki wani kauyen a Taraba

Sojoji 6 sun kwanta dama yayin da yan bindiga suka farmaki wani kauyen a Taraba

  • Tsagerun yan bindiga sun farmaki dakarun rundunar sojoji a kauyen Tati da ke karamar hukumar Takum ta jihar Taraba
  • A yayin harin, maharan sun halaka dakarun soji shida sannan suka yi awon gaba da wani babban jami'i
  • A yanzu haka, rundunar sojin na nan tana gudanar da bincike da aikin ceto jami'inta da aka sace a harin

Taraba - Rahotanni sun kawo cewa sojoji shida sun mutu a wani hari da yan bindiga suka kai kauyen Tati da ke karamar hukumar Takum ta jihar Taraba.

An tattaro cewa yan bindigar sun zo ne da yawansu sannan suka farmaki kauyen a ranar Talata da misalin 10 na dare.

Jaridar The Cable ta rahoto cewa maharan sun fafata da dakarun bataliya ta 93 a wani musayar wuta.

Sojoji 6 sun kwanta dama yayin da yan bindiga suka farmaki wani kauyen a Taraba
Sojoji 6 sun kwanta dama yayin da yan bindiga suka farmaki wani kauyen a Tarabab Hoto: channelstv.com
Asali: UGC

Sai dai yan bindigar sun sha karfin yan ta’addan, inda suka kashe sojoji shida da sace wani babban jami’i daya.

Kara karanta wannan

Ta'addanci: 'Yan ta'adda sun bindige jami'an 'yan sanda har 3 a jihar Neja

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Rundunar sojin ta bayyana Dauda Tata (7NA/44/4046), Yusuf Salihu (95NA/42/6911), Ndubuise Okonkwo (96NA/42/6911), Abdullahi Ibrahim, Emmanuel Jerrry (14NA/72/14051) da Sani Isa a matsayin wadanda suka mutu.

Majiyoyin soji sun ce yan bindigar sun kuma yi kautan bauna sannan suka farmaki sojin da aka turo daga Marraraba, amma dakarun suka mayar masu da martani.

Majiyoyin sun ce an kashe yan bindiga biyu yayin da sauran suka tsere da raunukan harbi.

Dakarun sun samo bindigar AK-47 daya, mujallar AK-47 guda biyu, karamin bindiga daya, bindigar gargajiya daya, layu da kudi N15,120.

Rahoton ya kuma bayyana cewa a yanzu haka ana nan ana gudanar da aikin bincike da ceto jami’in da aka sace.

Sama da tubabbun 'yan ta'adda 51,000 da iyalansu ke hannunmu, Rundunar sojin Najeriya

A wani labari na daban, mun ji cewa fiye da tubabbun 'yan ta'adda 51,000 da iyalansu ne suka zub da makamansu ga sojojin yankin Arewa maso Gabas kamar yadda sojojin suka bayyana.

Kara karanta wannan

An kama wani Soja da ke sayarwa yan bindiga makamai a Zamfara, ya yi bayani dalla-dalla

Kwamandan rundunar operation Hadin Kai, Manjo Janar Chris Musa, ya bayyana wa Channels TV yayin tattaunawar da suka yi da shi a ranar Litinin.

Ya bayyana yadda mazauna yankin suka dinga taimakon sojoji, musamman yadda suka samu bayanan sirri duk da cewa akwai bangaren da aka sanya wa shamakin sadarwa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel