Hatsabibin shugaban 'yan bindiga, Leggi Jibrin, ya shiga hannun sojojin Najeriya

Hatsabibin shugaban 'yan bindiga, Leggi Jibrin, ya shiga hannun sojojin Najeriya

  • Hatsabibi kuma gagararren shugaban 'yan bindiga da ya addabi jihohin Benue, Nasarawa da Taraba ya shiga hannun hukuma
  • Rundunar OPWS ta sojin Najeriya ta tabbatar da damke Leggi Jibrin da ta yi a kauyen Gidan Bawa da ke Nasarawa
  • An samu nasarar ceto mutum 5 daga sansanin 'yan bindiga da ke dajin Zaure bayan samamen da zakakuran dakarun suka kai

Nasarawa - Fitaccen gagararren shugaban kungiyoyin ta'addancin da suka addabi yankunan jihohin Benue, Nasarawa da Taraba, Leggi Jibrin, ya shiga hannun jami'an tsaro bayan artabun musayar wuta da yayi da dakarun sojin rundunar Operation Whirl Stroke, rundunar tsaro ta hadin guiwa dake kula da jihohin uku.

Vanguard ta ruwaito cewa, an tattaro daga bakin majiyar tsaro, cewa dan bindigan da OPWS ta dade tana nema ya shiga hannun sojoji ne a kauyen Agam/Gidan Bawa dake karamar hukumar Nasarawa ta jihar Nasarawa yayin da suka fita aiki.

Kara karanta wannan

Zaɓen 2023: Kada Ka Ruɗa Ƴan Najeriya, Ƙungiya Ta Ja Kunnen Atiku

Hatsabibin shugaban 'yan bindiga, Leggi Jibrin, ya shiga hannun sojojin Najeriya
Hatsabibin shugaban 'yan bindiga, Leggi Jibrin, ya shiga hannun sojojin Najeriya. Hoto daga dailytrust.com
Asali: Twitter

Majiyar ta ce dakarun sun yi aikin ne a ranakun Laraba da Alhamis karkashin umarnin kwamandan rundunar, Manjo Janar Kevin Aligbe. Hakan yayi sanadiyyar ceto mutum biyar da aka yi garkuwa da su a Ugya dake karamar hukumar Toto ta jihar.

Kamar yadda majiya daga dakarun ta bayyana, "Sojojin OPWS da aka tura Ugya dake karamar hukumar Toto ta jihar Nasarawa sun samu gamsassun bayanai kuma suka hanzarta kai dauki bayan samu kiran da suka yi kan cewa an yi garkuwa da wasu mutane kuma an kai su dajin Zaure.
"Daga isar su dajin, dakarun sun tarar da manyan motoci uku dankare da timber wacce aka diba ba bisa ka'ida ba kuma aka bar su a dajin. Kamar yadda dakarun suka ce, sun bincike dajin inda suka ci karo da sansanin masu garkuwa da mutane kuma suka ceto mutum biyar."

Kara karanta wannan

Miyetti Allah: Ƴan Bindiga Sunyi Garkuwa Da Mambobinmu 10 Da Shanu 300, Sun Buƙaci N4m Da Bindiga Ɗaya a Anambra

"Wadanda aka ceto su ne Abdulkafar Nuhu, Adamu Dagana, Emmanuel Osased, Jacob Amaku da Danladi Amaku.
"A yayin aikin, dakarun sun cafke hatsabibin mai garkuwa da mutane a kauyen Agam/Gidan Bawa dake karamar hukumar Nasarawa a jihar Nasarawa.
"'Yan bindigan suna tsaka da kai farmaki yankin yayin da OPWS suka dakile su. An yi ruwan wuta tsakaninsu da dakarun wanda yayi sanadin kama Jibrin tare da halaka daya daga cikin 'yan bindigan.
"A yayin da jami'an mu suka shiga yankin da suka kai farmaki, wasu daga cikin 'yan bindigan dauke da miyagun makamai sun tsere yayin da suka hango jami'an.
"Daga nan dakarunmu suka fatattakesu inda suka yi musayar wuta. Hatsabibin, wanda aka harba a kafa ya shiga hannun mu kuma wasu sun sheka lahira.
"Dole ne in ce an samu nasarar samamen nan ne sakamakon bayanan sirri da muka samu kan cewa hatsabibin tare da mukarrabansu sun kai hari wasu kauyukan yankin."

Kara karanta wannan

2023: Kwana Kaɗan Bayan Buhari Ya Musu Afuwa, An Yi Kira Ga Dariye Da Nyame Su Fito Takarar Shugaban Ƙasa

Ya ce wasu daga cikin abubuwan da aka samu daga 'yan bindigan sun hada da bindiga kirar AK-47 daya, AK-49 daya, harsasai masu rai 106 tare da wayar tafi da gidanka, Vanguard ta tattaro.

Kokarin jin ta bakin mai magana da yawun OPWS, Flying Officer Audu Katty ya gagara.

Katsina: 'Yan sanda sun halaka 'yan ta'adda 2, sun ceto wasu da aka yi garkuwa da su

A wani labari na daban, rundunar 'yan sandan jihar Katsina ta yi nasarar sheke a kalla 'yan ta'adda guda biyu, tare da gano makamansu, kayan sihirce-sihircensu da abubuwa masu fashewa a ranar Alhamis.

Channels TV ta ruwaito cewa, kakakin 'yan sandan, Gambo Isah, ya sanar da hakan yayin tattaunawa da manema labarai a hedkwatar rundunar a Katsina.

Asali: Legit.ng

Online view pixel