Yanzun nan: Sanatan APC Okorocha ya karbi fom din takarar shugaban kasa a zaben 2023

Yanzun nan: Sanatan APC Okorocha ya karbi fom din takarar shugaban kasa a zaben 2023

  • Sanatan APC daga yankin Kudu, Rochas Okorocha ya sayi fom din takarar shugaban kasa a jam'iyyar APC mai mulki
  • Okorocha ne ya bayyana hakan ta shafinsa na Facebook da yammacin yau Juma'a, kamar yadda wakilinmu ya samu
  • Okorocha dai ya shiga jerin wadanda suka karbi fom din takara gabanin taron zaben fidda gwani da PDP za ta yi nan kusa

A yau ne kungiyar TNN ta samarwa da sanata Rochas Okorocha fom din nuna sha'awa da tsayawa takarar shugaban kasa a jam'iyyar APC.

Hakan na zuwa ne daidai lokacin da jiga-jigan jam'iyyar APC ke ci gaba da biyan makuda milliyoyi domin nuna sha'awarsu da gaje kujerar shugaba Buhari.

Okorocha ya karbi fom din gajeBuhari
Shirin 2023: Okorocha ya karbi fom din takarar shugaban kasa na APC | Hoto: Senator Rochas Okorocha
Asali: Facebook

A wata sanarwar da ya fitar ta shafinsa na Facebook, Okorocha ya bayyana cewa, a yau karbi fom din ne a yau Juma'a 29 ga watan Afrilu, inda ya ce:

Kara karanta wannan

2023: Shugaban APC Ya Bayyana Dalilan Saka N100m a Matsayin Kudin Fom Din Takarar Shugaban Kasa

"Da yammacin yau ne aka mika min fom din tsayawa takarar shugaban kasa a zaben 2023 karkashin inuwar jam’iyyar All Progressives Congress daga kungiyar The New Nigeria (TNN)."

Hakazalika, ya sake jaddada manufarsa ta siyasa, tare da cewa, yana nan kan bakansa na tabbatar da kai Najeriya ga tudun mun tsira idan aka bashi dama a zaben 2023 mai zuwa idan Allah ya kaimu.

A duban da Legit.ng Hausa ta yi, hotuna sun nuna Okorocha cikin farin ciki yayin da yake karbar fom a hannun wasu jiga-jigai daga Kudu da ma Arewacin Najeriya.

2023: An karba wa Tinubu fom din takarar shugaban kasa na jam'iyyar APC

A wani labarin na daban, kun ji cewa, tsohon gwamnan jihar Legas, Bola Tinubu, ya karbi fom din N100m na jam’iyyar APC domin nuna sha'awa da tsayawa takarar shugaban kasa, kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Kowa tashi ta fishe shi: Shugaban PDP ya nunawa Atiku ba sani ba sabo

Vanguard ta ruwaito cewa, jiga-jigan kungiyar goyon bayan Tiubu ta TSG ce ta dura cibiyar taron kasa da kasa ICC domin sayen fom din a madadin Tinubu.

An tattaro cewa Tinubu, wanda ya tafi kasar Saudiyya aikin Hajji, ya samu wakilcin wasu makusantan sa da suka hada da dan majalisar wakilai daga mazabar tarayya ta Ikeja, James Faleke.

Asali: Legit.ng

Online view pixel