Katsina: 'Yan sanda sun dakile harin 'yan bindiga, sun ceto wasu mata, sun kwato AK47

Katsina: 'Yan sanda sun dakile harin 'yan bindiga, sun ceto wasu mata, sun kwato AK47

  • Rundunar 'yan sandan jihar Katsina ta ceto wasu mutanen da aka sace, ta kuma fattaki wasu 'yan bindiga
  • A yayin wani aikin, an hallaka wani kasugumin dan bindiga a lokacin da suka kai hari kan mazauna
  • Rundunar ta kuma bayyana irin nasarorin da jami'anta suka samu a cikin mako guda a cikin jihar ta Kastina

Katsina - Rundunar ‘yan sandan jihar Katsina, a ranar Alhamis, ta tabbatar da mutuwar wani dan ta’adda a yayin wani artabu a kauyen Marina da ke karamar hukumar Safana a ranar Larabar da ta gabata.

Kakakin rundunar ‘yan sanda, SP Gambo Isah ne ya tabbatar da faruwar lamarin a wata sanarwa da ya fitar a yammacin ranar Alhamis, inji rahoton Punch.

Isah ya bayyana cewa ‘yan ta’addan sun kai farmaki kauyen ne da sanyin safiyar Laraba, inda mazauna kauyen suka aike da sakon barnar 'yan bindigan ga ‘yan sanda.

Kara karanta wannan

Kaduna: Ƴan Bindiga Sun Yi Garkuwa Da Basarake, Sun Buƙaci Man Fetur Da Katin Waya a Matsayin Kuɗin Fansa

Barnar 'yan bindiga a jihar Katsina: An kashe dan bindiga
Katsina: 'Yan sanda sun dakile harin 'yan bindiga, sun ceto wasu jama'a | Hoto: channelstv.com
Asali: UGC

A cewarsa, DPO a yankin ya jagoranci tawagar ‘yan sanda da ‘yan banga inda suka yi artabu da ‘yan ta’addan a wata fafatawa ta bindiga.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Rahotanni sun ce an fatattaki ‘yan ta’addan ne bayan da aka harbe daya daga cikinsu a fafatawar da suka yi da bindiga.

An kwato bindiga da babura daga hannun 'yan ta'adda

Kakakin rundunar ‘yan sandan ya kuma bayyana cewa, an kwato bindiga kirar AK47 guda daya da kuma babura guda biyu na ‘yan ta’addar.

Isah ya kuma yi magana game da sauran ayyukan ‘yan sanda a cikin makon, inda ya bayyana irin nasarori da jami'an suka samu a lokutan ayyukansu.

Daga ciki, Channels Tv ta ruwaito cewa, an kubutar da mata uku da aka yi garkuwa da su da shanu goma sha biyar (15) na mutanen wani kauye.

Kara karanta wannan

Nasara daga Allah: Sojoji sun kashe kwamandan ISWAP, sun ceto mutane 848 da aka sace

Kaduna: Ƴan Bindiga Sun Yi Garkuwa Da Basarake, Sun Buƙaci Man Fetur Da Katin Waya a Matsayin Kuɗin Fansa

A wani labarin, ‘Yan bindiga sun yi garkuwa da Ayuba Dakolo, dagacin kauyen Rijana da ke Jihar Kaduna da wasu manoman yankin sannan har sun bayyana abubuwan da su ke bukata a matsayin kudin fansa, Vanguard ta ruwaito.

An samu bayanai daga mazauna yankin akan yadda su ka kira waya su na bukatar man fetur, man injin da kuma sigari a matsayin kudin fansa.

A cewar majiyar: “Dagacin yana nan lafiya lau. Mun yi magana. ‘Yan bindigan sun kuma nemi katin waya. Sun ce za su halaka shi idan aka gaza tura musu kayan da su ka nema."

Asali: Legit.ng

Online view pixel