Kaduna: Ƴan Bindiga Sun Yi Garkuwa Da Basarake, Sun Buƙaci Man Fetur Da Katin Waya a Matsayin Kuɗin Fansa

Kaduna: Ƴan Bindiga Sun Yi Garkuwa Da Basarake, Sun Buƙaci Man Fetur Da Katin Waya a Matsayin Kuɗin Fansa

  • ‘Yan bindiga sun yi garkuwa da dagacin kauyen Rijana da ke cikin Jihar Kaduna, Ayuba Dakolo tare da wasu manoma kasancewar yankin yawanci manoma ne
  • An samu bayani akan yadda suka kira iyalin dagacin inda suka bukaci man fetur, man injin, sigari da kuma katin waya a matsayin kudin fansa
  • A cewar majiyar da ta sanar da manema labarai, ‘yan bindigan sun yi barazanar halaka dagacin matukar aka ki tura musu abubuwan da su ka nema

Kaduna - ‘Yan bindiga sun yi garkuwa da Ayuba Dakolo, dagacin kauyen Rijana da ke Jihar Kaduna da wasu manoman yankin sannan har sun bayyana abubuwan da su ke bukata a matsayin kudin fansa, Vanguard ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Yan bindiga sun sake garkuwa da Basarake a Kaduna, sun nemi abu biyu ko su kashe shi

Kaduna: Ƴan Bindiga Sun Yi Garkuwa Da Basarake, Sun Buƙaci Man Fetur Da Katin Waya a Matsayin Kuɗin Fansa
Kaduna: ‘Yan bindiga sun yi garkuwa da dagacin kauye, sun bukaci man fetur da katin waya a matsayin kudin fansa. Hoto: The Punch.
Asali: UGC

An samu bayanai daga mazauna yankin akan yadda su ka kira waya su na bukatar man fetur, man injin da kuma sigari a matsayin kudin fansa.

A cewar majiyar:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

“Dagacin yana nan lafiya lau. Mun yi magana. ‘Yan bindigan sun kuma nemi katin waya. Sun ce za su halaka shi idan aka gaza tura musu kayan da su ka nema.”

Kakakin rundunar ‘yan sandan Jihar Kaduna, Muhammad Jalige, bai riga ya ce komai ba dangane da lamarin.

Wata mata da su ka sace ta haihu a wurinsu

Ana tsaka da wannan ne ‘yan bindigan su ka saki hotunan jaririyar da wata mata mai juna biyu ta haifa a hannunsu wacce su ka sace bayan kai wa jirgin kasan Abuja zuwa Kaduna farmaki.

Kamar yadda Daily Trust ta rahoto, sun yi garkuwa da mai cikin ne a ranar 28 ga watan Maris din 2022 a lokacin tana da ciki mai watanni 8.

Kara karanta wannan

Da Ɗumi-Ɗumi: 'Yan Bindiga Sun Saki Hoton Jaririyar Da Matar Da Suka Sace A Jirgin Kasan Kaduna Ta Haifa

Matar daya ce daga cikin fasinjoji 63 da su ka sace. Kuma har yanzu mutum daya su ka saki, Alwan Hassan, Manajan Darekta na Bankin Noma, BOA, bayan ‘yan uwansa sun tura musu N100m a matsayin kudin fansa.

Wata majiya ta shaida wa manema labarai cewa, jiya ne wata daya cur da mummunan harin ya auku.

'Yan Ta'adda Sun Afka Wa Mutane a Masallaci Yayin Buɗe-Baki, Sun Kashe 3 Sun Sace Wasu Da Dama

A wani labarin, ‘yan bindiga sun kai farmaki masallaci inda suka afka wa wa mutane yayin da suke tsaka da yin buda-baki, wanda ya ja suka halaka mutane uku, Daily Trust ta ruwaito.

Daily Trust ta gano yadda ‘yan ta’addan suka isa da yawansu, har suka sace wasu da yawa a masallacin sannan suka zarce da su inda ba a sani ba.

An tattaro bayanai akan yadda lamarin ya auku a kauyen Baba Juli da ke karamar hukumar Bali a cikin Jihar Taraba.

Kara karanta wannan

Harin jirgin Abj-Kad: Daya daga cikin matan da aka sace ta haihu a hannun 'yan bindiga

Asali: Legit.ng

Online view pixel