Nasara daga Allah: Sojoji sun kashe kwamandan ISWAP, sun ceto mutane 848 da aka sace

Nasara daga Allah: Sojoji sun kashe kwamandan ISWAP, sun ceto mutane 848 da aka sace

  • Hukumar tsaron Najeriya ta bayyana yadda aka kame wasu jiga-jigan 'yan ta'adda a kasar nan yayin wasu ayyuka
  • An kuma ceto wasu mutane da dama da aka sace a wasu hare-haren 'yan ta'adda a yankunan Arewacin Najeriya
  • Hakazalika, an kashe wani kasurgumin kwamandan 'yan ta'addan kungiyar ISWAP tare da kame mai kawo musu bayanai

Najeriya - Hedikwatar tsaron Najeriya a ranar Alhamis ta sanar da cewa, a kalla mutane 848 da aka yi garkuwa da su ne sojoji suka kubutar a wani samame daban-daban a fadin kasar cikin makwanni uku da suka gabata.

Jaridar Punch ta rahoto cewa, da yake jawabi yayin wani taron manema labarai a Abuja, Daraktan ayyukan yada labarai na tsaro, Janar Benard Onyeuko, ya kuma ce sojoji sun kashe wani fitaccen kwamandan kungiyar ISWAP, Abubakar Dan-Buduma.

Kara karanta wannan

Tashin hankali yayin da 'yan bindiga sun kashe shugaban tsagin jam'iyyar APC a Bayelsa

Yadda sojoji suka yi aikin kakkabe 'yan ta'adda
Nasara daga Allah: Sojoji sun kashe kwamandan ISWAP, sun ceto mutane 848 da aka sace | Hoto: thecable.ng
Asali: Depositphotos

Ya kara da cewa an kuma kama masu kwarmato bayanai na ‘yan ta’addan a ayyuka daban-daban tsakanin 7 da 28 ga Afrilu, 2022.

Yadda lamurran suka faru

Onyeuko ya ce:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"Sojoji sun kashe 'yan ta'adda 23, sun ceto fararen hula 619, tare da kama 'yan ta'adda 19. Sojoji sun mayar da martani kan harin da ‘yan ta’adda suka kai a Wanzamai da ke karamar hukumar Tsafe a jihar Zamfara.
“Sojoji sun tsaftace kauyen inda suka yi artabu da ‘yan ta’addan, aka kashe ‘yan ta’adda da dama. A aikin, sojoji sun ceto mata 32 da kananan yara 18.
“Haka kuma, a lokacin aikin, sojojin sun kwato shanu 592 da aka sace. Sojojin sun kuma kubutar da fararen hula 179 tare da kashe 'yan ta'adda 62 tare da kama 'yan ta'adda 100.
“Sashen kasa na Operation Hadin Kai tare da goyon bayan dakaru na sama sun gudanar da wani samame a Arina Woje da ke karamar hukumar Marte a jihar Borno tare da kashe wani fitaccen kwamandan kungiyar ISWAP Abubakar Dan-Buduma da ‘yan ta’adda da dama.

Kara karanta wannan

Karin bayani: 'Yan bindiga sun kashe shugaban jam'iyyar APC a yankin Kaduna

“Har ila yau, an kama wani shahararren dan kwarmato bayanai ga kungiyar ISWAP Mallam Abba Sidi Lawan a garin Auno da ke karamar hukumar Konduga a jihar Borno.
“Hakazalika, sojoji sun kama Abdurrazaq Hudu wani mai sayar da kayan masarufi ISWAP a kauyen Mutum Biyu da ke karamar hukumar Gassol a jihar Taraba.”

Onyeuko ya kuma ce adadin ‘yan ta’adda 1,158 da iyalansu da suka hada da maza 164, mata 367 da yara 627 ne suka mika wuya ga sojoji a cikin makwanni uku da suka gabata.

Ya ce an mika dukkan kayayyakin da aka kwato, da ‘yan ta’addan da aka kama, an mika su ga hukumomin da suka dace domin daukar mataki.

A jimlace, an kwato litar danyen mai 7,732,000 da lita 10,821,605 na AGO a wasu ayyukan, kamar yadda Tori ta tattaro.

Hafsoshin tsaro sun dira Hedkwatar yan sanda kan harin jirgin kasa

A wani labarin, babban hafsan tsaron ƙasar nan, Janar Lucky Irabor, Sufeta Janar na yan sandan ƙasa, Usman Alkali Baba, da sauran shugabannin tsaro yanzu haka sun shiga taron sirri a Hedkwatar tsaro, Abuja.

Kara karanta wannan

ICPC ta fallasa dabarar da ‘Yan Majalisa su ke yi, su na yin awon gaba da dukiyar talakawa

Wannan taron dake gudana na ɗaya daga cikin yunƙurin da shugabannin hukumomin tsaro ke yi don kubutar da Fasinjojin jirgin ƙasan Kaduna-Abuja, waɗan da aka sace wata ɗaya kenan.

Wata majiya ta shaida wa Daily Trust cewa Hafsoshin tsaron na shan matsin lamba kan su tabbata sun kuɓutar da Fasinjojin kafin Eid-El-Fitr.

Asali: Legit.ng

Online view pixel