Da Dumi-Dumi: 'Yan Bindiga Sun Saki Hoton Jaririyar Da Matar Da Suka Sace A Jirgin Kasan Kaduna Ta Haifa

Da Dumi-Dumi: 'Yan Bindiga Sun Saki Hoton Jaririyar Da Matar Da Suka Sace A Jirgin Kasan Kaduna Ta Haifa

  • ‘Yan bindiga sun saki hoton jaririyar da wata mata mai ciki cikin fasinjojin jirgin kasan Kaduna zuwa Abuja da suka sace ta haifa a hannunsu
  • Idan ba a manta ba, ‘yan bindigan sun sace fasinjoji 63 ranar 28 ga watan Maris, wanda cikinsu har da wata mata mai dauke da juna biyu wanda ya kai watanni 8
  • Kwana biyu da suka gabata ne aka samu labarin haihuwar matar daga wata ‘yar uwarta, a ranar Laraba da yamma kuma ‘yan bindigan suka saki hoton jaririyar

Hotunan jaririyar da aka haifa a hannun ‘yan bindiga sun bayyana. Idan ba a manta ba mahaifiyarta tana daya daga cikin fasinjojin jirgin kasan Abuja zuwa Kaduna da ‘yan bindiga suka sace a ranar 28 ga watan Maris din 2022.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Nakiya ta fashe da sojoji a Katsina, ta kashe jami'ai 3, wasu sun jikkata

'Yan Bindiga Sun Saki Hoton Jaririyar Da Matar Da Suka Sace A Jirgin Kasan Kaduna Ta Haifa
'Yan Ta'adda Sun Saki Hoton Jaririyar Da Matar Da Suka Sace A Jirgin Kasan Kaduna Ta Haifa. Hoto: Nigerian Tribune
Asali: Twitter

A lokacin da aka sace su, matar tana dauke da juna biyu mai watanni 8. Kuma a cikin fasinjoji 63 da suka sace, manajan darektan Bankin noma (BOA), Alwan Hassan ne kadai suka saki bayan an biya su N100m na kudin fansa.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Wata daya kenan cur da satarsu, wata mata cikinsu ta haifi jaririya, Nigerian Tribune ta ruwaito.

A ranar Laraba da yamma wata kungiyar ‘yan ta’adda da ake zargin ta Ansaru ce, reshen Boko Haram ta saki hoton jaririyar.

Da alamu jaririyar tana cikin koshin lafiya

Kwana biyu kenan da suka gabata da samun labarin haihuwarta inda ya dinga bazuwa a kafafen sada zumunta bayan wata ‘yar uwar matar ta shaida cewa ta haihu a ranar karshen mako.

Duk da dai ba a bayyana ko diyar wacece jaririyar ba har sai ranar Laraba sannan ‘yan ta’addan suka saki hotunan ta.

Kara karanta wannan

Harin jirgin Abj-Kad: Daya daga cikin matan da aka sace ta haihu a hannun 'yan bindiga

An ga jaririyar sanye da wata riga mai kalar ruwan hoda da kuma hular sanyi mai kalar ruwan ganye yayin da alamu ke nuna tana cikin koshin lafiya kuma ana kulawa da ita.

Business Hallmark ta tattaro yadda ‘yan ta’addan suka gayyaci likita don ya amshi haihuwar.

Yan Ta'addan Da Suka Kai Hari Sansanin Sojoji Na Kaduna Sun Ɗanɗana Kuɗarsu, Lai Mohammed

A bangare gudan, Gwamnatin Tarayya, a ranar Laraba ta ce yan ta'addan da suka kai hari sansanin sojoji da ke Birnin Gwari a Kaduna sun sha azaba a hannun sojoji a yayin da suka fatattake su, rahoton Daily Trust.

Ministan Labarai da Al'adu, Alhaji Lai Mohammed, ne ya bayyana hakan yayin da ya ke amsa tambayoyi kan tsaro bayan taron FEC da Shugaba Muhammadu Buhari ya jagoranta a Aso Villa a Abuja.

Rahotanni sun bayyana cewa sojoji 11 ne suka riga mu gidan gaskiya yayin da wasu da dama suka jikkata yayin harin na ranar Talata.

Kara karanta wannan

Harin jirgin kasa Abuja-Kaduna: Yan bindiga sun saki hotunan mutane 62 da suka sace

Asali: Legit.ng

Online view pixel