Yanzu-Yanzu: Nakiya ta fashe da sojoji a Katsina, ta kashe jami'ai 3, wasu sun jikkata

Yanzu-Yanzu: Nakiya ta fashe da sojoji a Katsina, ta kashe jami'ai 3, wasu sun jikkata

  • Labarin da muke samu daga jihar Katsina ya bayyana cewa, wata nakiya ta tashi da wasu sojojin Najeriya
  • Rahoton da ya bayyana cewa, alalla mutane uku ne suka mutu yayin da wasu suka samu raunuka da dama
  • Ya zuwa yanzu dai hukumomi basu tabbatar da faruwar wannan mummunan lamari ba ga manema labarai

Jihar Katisna - Akalla jami’an sojin Najeriya uku ne suka rasa rayukansu a wata tashin nakiya da ‘yan ta’adda suka binne a karamar hukumar Danmusa ta jihar Katsina.

Wata majiyar soji ta shaidawa jaridar Leadership cewa, dakarun na kan wani samame na musamman ne a unguwar Kaiga lokacin da daya daga cikin motocinsu ya taka wata nakiya da ‘yan ta’addan suka binne.

Yadda nakiya ta tashi da sojoji a Katsina
Yanzu-Yanzu: Nakiya ta fashe da sojoji a Katsina, ta kashe jami'ai 3, wasu sun jikkata | Hoto: thenationonlineng.net
Asali: UGC

Majiyar ta kuma ce an garzaya da wasu da suka jikkata zuwa wani asibiti a Katsina domin kula da lafiyarsu.

Kara karanta wannan

Karin bayani: 'Yan bindiga sun kashe shugaban jam'iyyar APC a yankin Kaduna

Majiyar ta ce:

“Suna kan hanyarsu ne daga Mara zuwa Kaiga kafin ‘yan bindigar da suka dasa nakiyar a Kaiga suka yi musu kwanton bauna. Jimillar sojoji uku ne suka mutu. Daya daga cikinsu ya kone tare da motar sintirin. An kai wadanda suka jikkata da wadanda suka mutu a harin zuwa BMC Kastina.
“An kwashe KIA da WIA zuwa BMC Katsina. An dasa na'urar EOD zuwa yankin don dubawa, amma ba a sami wani nakiyar IED ba."

Ba a samu damar samun jin ta bakin Daraktan yada labarai na tsaro, Manjo Janar Jimmy Akpor ba, har zuwa lokacin hada wannan rahoto.

Hakazalika daraktan ayyukan yada labarai na tsaro, Manjo Janar Benard Onyeuko, shi ma ba a same shi ba, amma shaidun bidiyo daga majiyoyin sun nuna aukuwar lamarin.

Kara karanta wannan

ICPC ta fallasa dabarar da ‘Yan Majalisa su ke yi, su na yin awon gaba da dukiyar talakawa

Yadda sojojin Najeriya suka ragargaji 'yan ta'addan Boko Haram a jihar Borno

Rundunar sojin Najeriya ta fitar da wasu hotunan da ke nuna yadda ta lalata mafakar 'yan ta'addan Boko Haram/ISWAP a yankin Kasha Kasha ta jihar Borno a yau Talata, 26 ga watan Afrilu.

Wannan na zuwa ne daidai lokacin da rundunar ke kara kaimi wajen dakile munanan ayyukan 'yan ta'adda a Arewancin Najeriya.

Rundunar ta ce, dakarun bataliya ta 195 tare da mambobin CTJTd ne suka yi wannan aiki a wani samamen da suka kai kan 'yan ta'addan.

Hotunan da Legit.ng Hausa ta samo daga shafin Twitter na Rundunar Sojin Najeriya sun nuna alamar gawargwakin 'yan ta'addan da kuma kayayyakin da aka lalata.

Gwamnan Zamfara ya tsige manyan sarakuna 2, da hakimi bisa taimakawa 'yan bindiga

A wani labarin, gwamnatin jihar Zamfara ta tsige wasu sarakuna biyu da hakimi daya bisa zargin taimaka wa ayyukan ta'addancin ‘yan bindiga da ke addabar al’ummar jihar.

Kara karanta wannan

Akwai yiwuwar APC ta hana Amaechi, Ngige, Malami da wasu Ministoci yin takara

Ibrahim Dosara, Kwamishinan Yada Labarai na Jihar Zamfara ne ya bayyana hakan a ranar Laraba yayin da yake zantawa da manema labarai a karshen taron Majalisar Zartaswar Jihar a Gusau, babban birnin Jihar.

Wadanda hukuncin gwamnatin ya shafa sun hada da Sarkin Zurmi, Abubakar Atiku, Sarkin Dansadau, Hussaini Umar, da kuma Sulaiman Ibrahim wanda ya taba zama Hakimin Birnin Tsaba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel