Harin jirgin Abj-Kad: Daya daga cikin matan da aka sace ta haihu a hannun 'yan bindiga

Harin jirgin Abj-Kad: Daya daga cikin matan da aka sace ta haihu a hannun 'yan bindiga

  • Wata mata mai juna biyu ta haihu a hannun 'yan bindiga bayan shafe akalla kwanaki 30 a sansaninsu
  • Wannan na zuwa ne bayan da wasu 'yan bindiga suka sace mutane da dama a jirgin kasar Abuja-Kaduna a watan jiya
  • Rahotanni sun nuna yadda 'yan bindigan ke da hanyoyin shigo da likitoci da masu kula da lafiya cikin daji

Najeriya - Daya daga cikin mata biyu masu juna biyu cikin fasinjojin da aka yi garkuwa da su a harin da ‘yan ta’adda suka kai kan wani jirgin kasa da ke kan hanyar Kaduna a watan da ya gabata ta haifi jariri a sansanin 'yan ta'adda.

Hakazalika, 'yan ta'addan da suka kai hari tare da yin garkuwa da fasinjojin sun fitar da hotuna daban-daban guda hudu na wadanda abin ya shafa da adadinsu ya kai akalla 62, inji rahoton This Day.

Kara karanta wannan

Karin bayani: 'Yan bindiga sun kashe shugaban jam'iyyar APC a yankin Kaduna

Yadda mata ta haihu a hannun 'yan bindiga
Harin jirgin Abj-Kad: Daya daga cikin matan da aka sace ta haihu a hannun 'yan bindiga | Hoto: thenationonlineng.net
Asali: UGC

A ranar 28 ga watan Maris ne ‘yan bindigar suka yi wa jirgin kasan da ke kan hanyarsa ta zuwa Kaduna daga babban birnin kasar kwanton bauna, inda suka tada bam a hanyarsa.

Tsagerun sun dage cewa ba dan kudin fansa suka yi aika-aikar ba, sai dai don a yi musayar fasinjojin da aka sace da wasu kwamandojinsu da ake zargin suna hannun gwamnati.

Yadda mata ta haihu a hannun 'yan bindiga

Wata majiya mai tushe ta tabbatar wa da tashar yada labarai ARISE News cewa daya daga cikin mata biyu masu juna biyu da aka yi garkuwa da su, ta haihu a sansanin ‘yan ta’addan tare da taimakon wasu likitocin da ‘yan ta'addan suka kawo.

Majiyoyi sun ce ‘yan ta’addar na da tsari da hadin kai ganin yadda suke iya samun shigar da kayayyakin jinya cikin dajin, al’amarin da suka bayyana a matsayin mai ban mamaki tsakanin jami’an gwamnati da na tsaro.

Kara karanta wannan

ICPC ta fallasa dabarar da ‘Yan Majalisa su ke yi, su na yin awon gaba da dukiyar talakawa

Wata majiya mai tushe ta rawaito cewa mata mai juna biyu daga cikin fasinjojin jirgin da aka sace ta haihu a karshen mako.

Matar da aka ruwaito tana dauke da ciki wata takwas a lokacin da aka sace su, ta haihu lafiya tare da samun kulawar likita.

Harin jirgin kasan Abuja-Kaduna: Yan bindiga sun saki hotunan mutane 62 da suka sace

A wani labarin, wata guda cir bayan harin da yan bindiga suka kai jirgin kasan Abuja-Kaduna inda akalla mutum 9 suka hallaka, yan ta'addan sun saki hotunan fasinjojin dake hannunsu.

Wata Lakcara a jami'ar jihar Kaduna, Bilkisu Yero, ce ta saki hotunan a shafinta na Facebook.

Hotunan da aka saki ranar Litinin ne karo na uku yan bindigan zasu saki bidiyo ko hoto dake nuna cewa wadanda suka sace na raya cikin lafiya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel