Yajin Aiki: Ƴan Siyasan Najeriya Sun Fi Boko Haram Hatsari, In Ji SSANU

Yajin Aiki: Ƴan Siyasan Najeriya Sun Fi Boko Haram Hatsari, In Ji SSANU

  • Kungiyar manyan ma'aikatan jami'o'in Najeriya, SSANU, reshen Yamma ta zargi FG da nuna ko in kula da batun ilimi a Najeriya
  • SSANU ta ce gwamnatin tarayyar ta fi kungiyar Boko Haram sharri wurin hana yaran talakawan Najeriya samun ilimin boko saboda rashin daukan matakan ganin an bude makarantu
  • Kungiyar manyan ma'aikatan jami'o'in ta kuma yi ikirarin cewa Ministan Kwadago Chris Ngige bai damu ya san dalilan da yasa suka tafi yajin aikin ba

Ibadan, Jihar Oyo - Kungiyar manyan ma'aikatan jami'o'in Najeriya, SSANU, ta zargi Gwamnatin Tarayya ta yaudara da rashin damuwa da samar da ingantaccen ilimi ga yan Najeriya, rahoton The Punch.

Kwamitin shugabannin SSANU na yankin Yamma, a ranar Laraba ta furta hakan yayin taron da ta yi a Ibadan, tana mai cewa yan siyasan Najeriya sun fi Boko Haram muni a bangaren hana yaran talakawa samun ilimi.

Kara karanta wannan

Yajin Aikin ASUU: Jami'ar Jihar Kaduna Ta Umurci Ɗalibai Da Malamai Su Koma Makaranta Bayan Sallah

Yajin Aiki: Ƴan Siyasa Najeriya Sun Fi Boko Haram Hatsari, In Ji SSANU
Yajin Aiki: Ƴan Siyasa Najeriya Sun Fi Boko Haram Sharri, In Ji SSANU. Hoto: The Punch.
Asali: Twitter

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Mataimakin shugaban SSANU na kasa, Dr Abdussobur Salaam, da Sakataren Yankin, wanda suka yi magana a madadin kungiyar sun ce rashin cika alkawarin da ke yarjejeniyar da suka yi da gwamnati tun 2009 na cikin dalilan da yasa suka tafi yajin aikin.

Ya ce:

"SSANU reshen Yamma sun nuna tarayya da shugabanninsu na kasa wurin shiga yajin aikin duk da cewa ba abu bane mai dadi musamman tunda an tsayar da albashinsu.
"Amma idan muna harka da gwamnati kurma kuma bebe, ya zama dole mu nemi kowanne hanya da za mu sanar da damuwarmu. Idan Boko Haram na nufin karatun boko haramun ne, babu wata kungiya da ke nuna boko haramun ne fiye da yan siyasan Najeriya.
"Fiye da wata shida, mun sanar za muyi yajin aiki, mun sha aika wasika amma ba bu wani amsa. Mun yi yajin aikin gargadi na sati biyu, babu amsa. Mun kara sati biyu, har yanzu babu amsa daga Ma'aikatar Ilimi ko Ma'aikatar Kwadago."

Kara karanta wannan

Karin bayani: 'Yan bindiga sun kashe shugaban jam'iyyar APC a yankin Kaduna

Ministan Kwadago Chris Ngige bai ma san dalilin da yasa muka tafi yajin aiki ba, SSANU

Kungiyar ta kuma soki Ministan Kwadago, Chris Ngige, wanda Salaam ya ce bai san abubuwan da ya tilasta manyan ma'aikatan jami'o'in shiga yajin aiki ba.

Ya ce Ngige ya bada amsa ka dallin zuwan SSANU yajin aiki da cewa kawai sun tafi yajin aikin ne domin ASUU sun tafi yajin aiki.

SSANU ta ce daga cikin dalilan zuwansu yajin aikin shine batun IPPIS da suka ce yaudara ce. Sauran dalilan sun hada da rashin samar da kudaden tafiyar da jami'o'i, kudin ritaya na mambobi da sauransu.

Yajin Aikin ASUU: Jami'ar Jihar Kaduna Ta Umurci Ɗalibai Da Malamai Su Koma Makaranta Bayan Sallah

A bangare guda, mahukunta a Jami'ar Jihar Kaduna, KASU, sun shirya fara zangon karatu na 2020/2021 a ranar 9 ga watan Mayu, Channels TV ta rahoto.

Jami'ar, cikin sanarwar da ta fitar mai dauke da kwanan watan 26 ga watan Afrilu da sa hannun sakataren harkokin karatu, Abdullahi Zubairu, ta umurci dalibai da malaman makarantar su cigaba da karatu.

Kara karanta wannan

Karin bayani: Yan bindiga sun sace wata mai taimakon talakawa da diyarta a Kaduna, sun nemi a biya N100m

Sanarwar ta kuma shawarci dukkan malamai da daliban jami'ar su yi biyayya ga tsarin karatun makarantar kamar yadda Information Nigeria ta rahoto.

Asali: Legit.ng

Online view pixel