Karin bayani: Yan bindiga sun sace wata mai taimakon talakawa da diyarta a Kaduna, sun nemi a biya N100m

Karin bayani: Yan bindiga sun sace wata mai taimakon talakawa da diyarta a Kaduna, sun nemi a biya N100m

  • Masu garkuwa da mutane sun sace wata mata da ke aikin tallafawa marasa karfi, Ramatu Abarshi da diyarta
  • An sace su ne jim kadan bayan sun gama rabawa al'umma kayan fitan Sallah a garin Mariri da ke karamar hukumar Lere ta jihar Kaduna
  • Kakakin rundunar yan sandan jihar Kaduna, Mohammed Jalige, ya ce bai da labarin faruwar al'amarin

Kaduna - Yan bindiga sun yi garkuwa da wata mai aikin taimakon jama’a, Ramatu Abarshi, da diyarta Amira, bayan sun gama raba kayan fitan sallah ga al’umman garin Mariri da ke karamar hukumar Lere ta jihar Kaduna.

Wata majiya ta kusa da iyalan ta sanar da cewa yan bindigar sun farmake su ne a ranar Asabar da rana a kusa da Kasuwan Magani da ke karamar hukumar Kachia, a yankin kudancin Kaduna, Daily Nigerian ta rahoto.

Kara karanta wannan

Yan bindiga sun sace makiyaya 10 da shanu 300 a jihar Anambra

Yan bindiga sun sace wata mata da diyarta jim kadan bayan sun gama rabawa jama’a kayan azumi a Kaduna
Yan bindiga sun sace wata mata da diyarta jim kadan bayan sun gama rabawa jama’a kayan azumi a Kaduna Horo: Daily Nigerian
Asali: UGC

Misis Abarshi, tsohuwar shugabar sashen Injiniyan Lantarki na kwalejin jihar Kaduna, ta yi suna sosai wajen aikin taimakon jama'a da shirin zaman lafiya a kudancin Kaduna.

Da aka tuntube shi, kakakin rundunar yan sandan jihar Kaduna, Mohammed Jalige, ya ce bai da labarin faruwar lamarin.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ya ce:

“Kun san mutane basa kaiwa yan sanda rahoton irin wannan lamari a nan take.”

Jaridar Punch ta rahoto cewa, wata majiya ta kusa da iyalan ta ce yan bindigar sun tuntube iyalan sannan sun bukaci a biya naira miliyan 100 a matsayin kudin fansarsu.

Zuwa yanzu dai gwamnatin jihar bata yi martani a kan al'amarin ba.

Yan bindiga sun sace makiyaya 10 da shanu 300 a jihar Anambra

A wani labarin, mun kawo cewa wasu yan bindiga da ake zaton masu garkuwa da mutane ne sun yi awon gaba da mambobin kungiyar Miyetti Allah guda 10 a yankin karamar hukumar Ogbaru da ke jihar Anambra.

Kara karanta wannan

Yan bindiga sun hallaka jami’an yan sanda 3 a wani farmaki da suka kai ofishinsu a Kogi

Jaridar The Cable ta rahoto cewa lamarin ya afku ne a rugar makiyaya da ke garin Obene a ranar Asabar, 23 ga watan Afrilu.

An kuma tattaro cewa maharan sun sace kimanin shanaye guda 300 mallakar makiyayan.

Asali: Legit.ng

Online view pixel