2023: Osinbajo Ya Gama Biyan Sadaki, Ya Cancanta Ya Zama Sabon Angon Nigeria, In Ji Basaraken Ƙasar Yarbawa

2023: Osinbajo Ya Gama Biyan Sadaki, Ya Cancanta Ya Zama Sabon Angon Nigeria, In Ji Basaraken Ƙasar Yarbawa

  • Oba Adedotun Gbadebo, Alake na kasar Egba, a Jihar Ogun ya ce mataimakin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo ya cancanci zama shugaban kasa a 2023
  • Basaraken na Yarabawa ya bayyana hakan ne yayin da Osinbajo da Gwamna Dapo Abiodun suka kai masa ziyara a fadarsa
  • Osinbajo a jawabinsa ya ce ya ziyarci sarkin ne domin ya yi masa bayani game da nasarorin da ya ke samu a takararsa na shugaban kasa

Ogun - Alake na kasar Egba, a Jihar Ogun, Oba Adedotun Gbadebo ya ce mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo ya yi biyayya don haka ya cancanci a zabe shi shugaban kasa a 2023, PM News ta ruwaito.

Vanguard ta rahoto cewa Gbadebo ya yi wannan jawabin ne a ranar Talata, a lokacin da ya karbi bakuncin mataimakin shugaban kasar da ya kai masa ziyarar ban girma.

Kara karanta wannan

2023: An rabawa Gwamna hankali a APC, a karshe ya zabi Osinbajo a kan Bola Tinubu

2023: Osinbajo Ya Gama Biyan Sadaki, Ya Cancanta Ya Zama Sabon Angon Nigeria, In Ji Basaraken Ƙasar Yarbawa
Osinbajo ya yi biyayya, ya kamata ya zama shugaban kasa na gaba, Oba Adedotun. Hoto: Vannguard.
Asali: Twitter

Osinbajo, wanda ya samu rakiyar Gwamna Dapo Abiodun na jihar Ogun ya tafi jihar ne domin tuntubar masu ruwa da tsaki game da takarar shugabancin kasarsa na 2023.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Basaraken ya ce Osinbajo ya sadaukar da kansa wurin yi wa kasa hidima kuma ya cancanci ya zama shugaban kasa na gaba.

Wani bangare cikin abin da basaraken ya ce:

"Duk shugaban kasa daga wannan yankin da ya ziyarci fadar nan ya yi nasarar zama shugaban kasa.
"Duk mataimakin shugaban kasa da ya ziyarci nan domin yin takara, ya yi nasara; wannan ba zai banbanta da sauran ba.
"Da izinin Allah, mataimakin shugaban kasar mu ya yi biyayya; ya yi wa na gaba da shi biyayya kuma ya yi nasara."

Daga karshe, ya yi addu'a cewa ziyarar da Osinbajo zai sake kawo wa fadar ta godiya ce bayan ya yi nasarar lashe zabe.

Kara karanta wannan

2023: Yahaya Bello Ya Shige Gaban Su Tinubu, Ya Fara Biyan N100m Lakadan Kuɗin Fom Ɗin Takara

Abin da Osinbajo ya fada a fadar Oba Adedotun Gbadebo

Tunda farko, Osinbajo ya ce ya taho fadar ne domin ya yi wa basaraken jawabi kan nasarorin da ya yi kawo yanzu.

"Mai martaba ya san cewa a ranar 11 ga watan Afrilu, na kaddamar da takara ta neman kujerar shugaban kasar tarayyar Najeriya a hukumance.
"Bayan hakan, na tuntubi gwamnonin mu; na gana da yan majalisa kuma na fara ziyarar jiha daya zuwa biyu.
"Yau rana ce mai muhimmanci, na zo sanar da mai martaba, mahaifina, nasarar da na yi, kuma na san yana tare da ni a dukkan takarar da na yi," in ji shi.

Yahaya Bello: Ƙaruwar Masu Fitowa Takarar Shugaban Ƙasa Baya Bani Tsoro Ko Kaɗan

A bangare guda, dan takarar shugaban kasa kuma Gwamnan Jihar Kogi, Yahaya Bello ya ce ko fargaba ba ya yi akan yadda mutane da dama suke ta fitowa takarar shugaban kasa, The Punch ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Martanin yan Najeriya kan sabuwar wakar sukar gwamnatin Buhari da Rarara ya yi

Haka zalika, ya ce bai tsorata ba da shirye-shiryen yarjejeniyar jam’iyya ba saboda yana sa ran kasancewa mai nasara a ko wanne irin mataki jam’iyyar ta dauka wurin zaben dan takara.

Ya bayyana hakan ne a wani taron manema labarai da Kungiyar Kamfen din shugabancin kasar Yahaya Bello ta shirya a Abuja.

Asali: Legit.ng

Online view pixel