ICPC ta fallasa dabarar da ‘Yan Majalisa su ke yi, su na yin awon gaba da dukiyar talakawa

ICPC ta fallasa dabarar da ‘Yan Majalisa su ke yi, su na yin awon gaba da dukiyar talakawa

  • Akwai dabaru iri-iri da Sanatoci da ‘Yan majalisa su kan yi domin su wawuri kudin mutanensu
  • Wasu su kan bada kwangila da nufin za a rabawa talakawa kaya, a karshe sai su sha kwana da kayan
  • Hukumar ICPC tayi wannan tonon sililin e a wani rahoton bincike da ta gudanar daga 2019 zuwa 2020

Abuja - Hukumar ICPC mai yaki da barayi a Najeriya ta ce wasu ‘yan majalisar tarayya a kasar nan sun gano salon sata da karkatar da dukiyar talakawansu.

Jaridar Daily Trust ta rahoto hukumar ta ICPC tana cewa ‘yan majalisa su kan bada sunan aikin mazaba na bogi, sai su maida dukiyar jama’a ta zama ta su.

ICPC ta bankado wannan asiri ne a wani rahoto da ta fitar kwanan nan mai taken ‘Constituency and Executive Projects Tracking Exercise Phase 3 Report’

Kara karanta wannan

Akwai yiwuwar APC ta hana Amaechi, Ngige, Malami da wasu Ministoci yin takara

Daga cikin yadda ‘yan majalisar ke yi, sai su ce za a kawo kayan tallafawa marasa karfi da abin hawa, ba tare da yin cikakken bayanin yadda za a raba su ba.

A karkashin wannan muguwar dabara, hukumar ta bada misalin awon gaba da wani ‘dan majliasa ya yi da na’urorin ban ruwa a mazabar kudancin Taraba.

‘Dan majalisar ya sa an shigo da wadannan kaya, amma bai rabawa mutanen da yake wakilta ba. A karshe sai aka iske kayan a hannun shi, ya saida su a kasuwa.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

'Yan Majalisa
Wasu Sanatoci a zaman majalisa Hoto: www.premiumtimesng.com
Asali: UGC

Binciken da hukumar kasar ta gudanar ya nuna mata an ware sama da Naira biliyan 100 a matsayin kudin ayyukan mazabu tsakanin shekarar 2019 da 2020.

Kwangilolin ci-mu-raba

Rahoton ya ce shugaban asibitin da ke maganin tarin tibi da kuturta da ke Zaria a jihar Kauna, ya saba bada kwangilolin bogi domin ya samu na shi kason kudin.

Kara karanta wannan

Sadau, Nafisa, ‘Yan wasan kwaikwayo 5 da suka taba tada kura a shafukan sada zumunta

A kan ba mutane kwangila ne ba tare da an bi dokar aiki ba, bayan nan sai a bukaci su dawowa shugaban asibitin wasu daga cikin kudin a matsayin ladar shi.

Majiyar ta ce tun farko dama an bada kwangilolin ne ba da nufin ayi aiki ba, sai domin a ci kudin. An samu kwangilolin bogi 16 irin wannan da suka ci N1.2bn.

A jihar Kano wani ‘dan majalisa ya ce zai raba motoci a mazabar Nasarawa, amma bai yi bayanin irin motocin da za a kawo ba, bai fadi abin da za a yi da su ba.

Wike ya raba N200m a Kaduna

A jiya ne aka ji Gwamna Nyesom Wike ya yi rabon N200m a Kaduna, ya bar tsofaffin ma’aikatan jihar Ribas su na kukan cewa rabonsu da fansho tun a 2014.

Mai neman takarar shugaban kasar ya roki ‘ya ‘yan jam’iyyar PDP na reshen jihar Kaduna su ba shi 80% na kuri’unsu a zaben fitar da gwani da za a gudanar.

Kara karanta wannan

Kin jinin Musulmi: China ta yi Allah wadai da wadanda suka kona al-Qur'ani a Sweden

Asali: Legit.ng

Online view pixel