Gwamnan Zamfara ya tsige manyan sarakuna 2, da hakimi bisa taimakawa 'yan bindiga

Gwamnan Zamfara ya tsige manyan sarakuna 2, da hakimi bisa taimakawa 'yan bindiga

  • Gwamnatin jihar Zamfara ta tsige sarakunan gargajiya biyu a jihar saboda zarginsu da hannun a lamurran 'yan bindiga
  • Wannan na zuwa ne bayan dakatar dasu da aka yi na tsawon watanni 10 har aka kammala bincike akansu
  • Yanzu dai an tsige su, gwamnati ta kuma bayyana mataki na gaba kan ayyukan da ake zarginsu dashi

Jihar Zamfara - Gwamnatin jihar Zamfara ta tsige wasu sarakuna biyu da hakimi daya bisa zargin taimaka wa ayyukan ta'addancin ‘yan bindiga da ke addabar al’ummar jihar.

Ibrahim Dosara, Kwamishinan Yada Labarai na Jihar Zamfara ne ya bayyana hakan a ranar Laraba yayin da yake zantawa da manema labarai a karshen taron Majalisar Zartaswar Jihar a Gusau, babban birnin Jihar.

An tsige sarakuna saboda taimakawa 'yan bindiga
Gwamnan Zamfara ya tsige manyan sarakuna 2, da hakimi bisa taimakawa 'yan bindiga | Hoto: channelstv.com
Asali: UGC

Wadanda hukuncin gwamnatin ya shafa sun hada da Sarkin Zurmi, Abubakar Atiku, Sarkin Dansadau, Hussaini Umar, da kuma Sulaiman Ibrahim wanda ya taba zama Hakimin Birnin Tsaba.

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: Gwamna ya ayyana neman ɗan majalisa ruwa a jallo, ya umarci a damƙe shi

Channels Tv ta ruwaito shi yana cewa:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

“Majalisar ta amince da tsige Sarkin Zurmi, Alhaji Atiku Abubakar, da na Dansadau, Alhaji Hussaini Umar.
“Majalisar ta kuma amince da tsige Hakimin Birnin-Tsaba, Alhaji Sulaiman Ibrahim nan take.”

A cewar kwamishinan, gwamnati ta kuma bayar da umarnin a soke duk wasu takardun mallakar fili da sarakunan gargajiyan suka bayar.

Ya kara da cewa:

"Majalisar zartaswar jihar ta kuma umarci ma'aikatar shari'a ta jihar da ta ba da umarnin zartarwa don tabbatar da kudurin majalisar."

Tsige sarakunan gargajiyar na zuwa ne watanni 10 bayan dakatar da su da gwamnatin jihar ta yi.

Hakan na zuwa ne kwanaki bayan mika rahoton kwamitocin da gwamnatin jihar ta kafa domin bincika zargin su da ake yi na hannun a ba 'yan bindiga kariya.

A kwanakin nan ne rahoton Premium Times ya bayyana yadda gwamnatin jihar ta gwangwaje sarakunan gargajiya da motocin alfarma watakila ko don dakile kulla alakarsu da 'yan ta'adda.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Majalisar dattawa ta haramta biyan masu garkuwa da mutane kudin fansa

Gwamnan Jihar Zamfara, Bello Matawalle ya dakatar da Sarkin Zurmi

A tun farko kun ji cewa, gwamnatin Jihar Zamfara ta dakatar da Sarkin Zurmi Alhaji Atiku Abubakar Muhammad daga kan karagar sarauta saboda zargin hannu a ayyukan ‘yan bindiga a masarautarsa.

Dakatarwar na zuwa ne bayan harin ranar Alhamis da ‘yan bindigar suka kai a kauyen Kadawa da ke masarautar inda suka kashe mutum 90.

Cikin wata sanarwa dauke da sa hannun Mukaddashin Sakataren Gwamnatin jihar, Alhaji Kabiru Balarabe, ta ce dakatarwar ta fara aiki nan take kuma an nada Alhaji Bello Suleiman (Bunun Kanwa) a zaman wanda zai tafiyar da al’amuran masarautar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel