N-Power: Matasa 13, 823 ne zasu amfana a rukunin C a jihar Filato, Sadiya Farouq

N-Power: Matasa 13, 823 ne zasu amfana a rukunin C a jihar Filato, Sadiya Farouq

  • Ministar jin ƙai da walwalar al'umma, Hajiya Sadiya Umar Farouq, ta ce matasa 13,823 zasu samu aikin yi a jihar Filato a tsarin N-Power
  • Ministar tace bayan umarnin shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, matasa da dama zasu samu shiga rukunin C
  • Ta yaba wa gwamnan jihar Filato, Simom Lalong, bisa ɗumbin goyon bayan da yake ba Agendar tsamo mutane daga talauci

Plateau - Ministan jin ƙai da walwalar al'umma, Sadiya Farouq, ta ce ma'aikatarta zata samarwa matasa 13,823 a jihar Filato ƙarƙashin shirin NSIP, na FG ayyukan yi.

Misis Farouq ta yi wannan furucin ne a wurin taron rufe horarwa da kuma ba da jalin farko ga waɗan da zasu ci gajiyar shirin N-Skills a Jos ranar Talata.

Daily Nigerian ta rahoto cewa Ministar ta samu wakilcin daraktan sashin shugabanci na ma'aikatar, Ladan Haruna. Ta ce za'a samar da aikin ne ta hanyar N-power rukunin C.

Kara karanta wannan

APC ta samu babban cikas, dubbannin masoyan Buhari sun koma bayan takarar Kwankwaso a 2023

Ministar jin ƙai da walwalar al'umma, Sadiya Farouq
N-Power: Matasa 13, 823 ne zasu amfana a rukunin C a jihar Filato, Sadiya Farouq Hoto: dailynigerian.com
Asali: UGC

A cewar Ministar jin ƙai an samu wannan cigaban ne biyo bayan amincewar shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, na ƙara faɗaɗa shirin N-Power matasa da dama su amfana.

A jawabinta, Misis Farouq ta ce:

"Ina mai ƙara jaddada kudirin shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, na yaƙar talauci da shawo ƙansa da kuma shawo kan zaman kashe wando tsakanin matasa ta hanyar shirin NSIP."
"Mun faɗaɗa ɓangaren masu karatu da waɗan da ba su yi karatu ba na shirin N-Power domin samar da damarmaki ga matasa 13,823 a jihar Filato kaɗai a rukunin C."
"Hakan ya biyo bayan samun nasarar gama cire matasa 11,505 a rukunin A da B. Bisa umarnin shugaban ƙasa zamu nunka waɗan nan damarmaki ga matasa."

Sadiya ta yaba wa gwamnan Filato

Kara karanta wannan

2023: Abinda zamu yi wa Bola Tinubu da a PDP yake neman shugaban ƙasa, Gwamnan Arewa

Daga ƙarshe ministan ta yaba wa gwamna Simon Lalong na jihar Filato bisa taimakawa agendar shugaba Buhari na tsamo yan Najeriya miliyan N100m daga ƙangin talauci.

A wani labarin kuma Rikicin APC a Kano, Sanata Shekarau ya yi magana kan batun ficewa daga jam'iyyar APC

Tsohon gwamnan Kano, Mallam Ibrahim Shekarau, ya musanta rahoton da ke yawo cewa yana shirin barin APC.

Shekarau mai wakiltar Kano ta tsakiya a majalisar Dattawa ya ce da su aka yanke wa APC cibiya, yanzun suna dakon hukuncin Kotun ƙoli.

Asali: Legit.ng

Online view pixel