2023: Da ace Tinubu a PDP yake shi zamu ba takara cikin sauki, Bala Muhammed

2023: Da ace Tinubu a PDP yake shi zamu ba takara cikin sauki, Bala Muhammed

  • Gwamna Bala Muhammed na Bauchi ya ce zasu ba Tinubu takara cikin maslaha da ace jam'iyya ya ba gudummuwa haka
  • Gwamnan ya ce ya haɗu da Tinubu a liyafar cin abincin buɗe baki da uwar gidan shugaban ƙasa ta shirya kuma sun tattauna
  • A cewar ɗan takarar shugaban ƙasan Bola Tinubu ya ba APC da Buhari gudummuwa, wacce ta kai su ga nasara a 2015

Abuja - Gwamnan jihar Bauchi, Bala Muhammed, ya ce da ace Bola Tinubu, (ɗan takarar shugaban ƙasa a APC), mamba ne a jam'iyyar PDP, da kowane ɗan takara ya hakura an miƙa masa tikitin takara a 2023.

Muhammed ya yi wannan furucin ne ranar Lahadi lokacin da ya bayyana a cikin wani shirin da aka haska kai tsaye jaridar Guardian ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Ruwan Zuma: An kashe mutum uku kan wata tsaleliyar budurwa a jihar Kwara

Gwamna Bala Muhammed na jahar Bauchi.
2023: Da ace Tinubu a PDP yake shi zamu ba takara cikin sauki, Bala Muhammed Hoto: @thecableng
Asali: Twitter

Gwamnan na ɗaya daga cikin yan takarar shugaban ƙasa da suka halarci liyafar cin abinci na buɗe baki da uwar gidan shugaban ƙasa, Hajiya Aisha Buhari, ta gayyace su ranar Asabar.

Abin da zamu yi wa Tinubu da a PDP yake takara - Muhammed

Da yake jawabi a cikin shirin, Muhammed ya ce ya haɗu da manyan mutanen ƙasar nan, inda ya ƙara da cewa da Tinubu a PDP yake da shi za su miƙa wa takara saboda gudummuwar da ya bayar.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

The Cable ta rahoto gwamnan yana cewa:

"Na samu damar haɗuwa da manyan mutane waɗan sa suka halarci wurin don nuna kan su. Na ci sa'ar ganin Asiwaju Bola Tinubu, har muka tattauna."
"Ya kira ni da sunan Sulhu, ni kuma na faɗa masa da a jam'iyyar PDP kake da mun baka tutar takara saboda mun san ba dan kai ba Buhari ba zai zama shugaban ƙasa ba, a PDP mun san halacci."

Kara karanta wannan

2023: Ya kamata Atiku ya janye mun saboda basira ta, Gwamnan Arewa dake mafarkin gaje Buhari

"Uwar gidan shugaban ƙasa tana son daidaito, ta nuna cewa ita ce uwar ƙasa, duk wani ɗan takara ba wai a PDP da APC ba kaɗai, kowa na wurin. Wata dama ce na samu ta nuna ni ɗan maslaha ne ba tare da duba jam'iyya ba."

A wani labarin kuma Malam Ibrahim Shekarau ya faɗi matsayarsa kan shirin ficewa daga jam'iyyar APC

Tsohon gwamnan Kano, Mallam Ibrahim Shekarau, ya musanta rahoton da ke yawo cewa yana shirin barin APC.

Shekarau mai wakiltar Kano ta tsakiya a majalisar Dattawa ya ce da su aka yanke wa APC cibiya, yanzun suna dakon hukuncin Kotun ƙoli.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262