Rikicin APC a Kano: Sanata Shekarau ya yi magana kan batun ficewa daga jam'iyyar APC

Rikicin APC a Kano: Sanata Shekarau ya yi magana kan batun ficewa daga jam'iyyar APC

  • Tsohon gwamnan Kano, Mallam Ibrahim Shekarau, ya musanta rahoton da ke yawo cewa yana shirin barin APC
  • Shekarau mai wakiltar Kano ta tsakiya a majalisar Dattawa ya ce da su aka yanke wa APC cibiya, yanzun suna dakon hukuncin Kotun ƙoli
  • A cewarsa, a ɓoye ko a fili ba ya shirin ficewa daga APC, kawai tsaginsa na jayayya ne da yadda ake tafiyar da jam'iyya

Kano - Sanata mai wakiltar Kano ta tsakiya a majalisar dattawan Najeriya, Malam Ibrahim Shekarau, ya ce yana nan daram a cikin jam'iyyar APC kuma ba shi da shirin sauya sheƙa.

Sanatan ya bayyana haka ne yayin da yake martani kan saƙonnin da mutane ke tura masa game da matsayarsa a jam'iyya mai mulki da kuma jita-jitar da ake jingina masa.

A wani rubutu da ya yi a shafinsa na Facebook, tsohon gwamnan Kano ya musanta raɗe-raɗin da ake yaɗa wa cewa yana shirin sauya sheƙa daga APC.

Kara karanta wannan

2023: Ya kamata Atiku ya janye mun saboda basira ta, Gwamnan Arewa dake mafarkin gaje Buhari

Tsohon gwamnan Kano, Sanata Ibrahim Shekarau.
Rikicin APC a Kano: Sanata Shekarau ya yi magana kan batun ficewa daga jam'iyyar APC Hoto: Mallam Ibrahim Shekarau/facebook
Asali: Facebook

A kalamansa, Shekarau ya ce:

"Ni, Sanata Ibrahim Shekarau, Sardaunan Kano, ina nan a jam'iyyar APC, babu wani shiri ko ƙulli a boye ko fili na sauya sheka zuwa wata jam'iyya ta daban."
"Ya kamata mutane su sani, da ni aka yanke wa jam'iyyar APC cibiya, kuma na yi aiki tuƙuru domin kafuwarta da nasararta."
"Yadda ake tafiyar da jam'iyyar ne muke jayayya a kai kuma maganar na gaban Kotu. Har yanzun muna sauraren hukuncin ƙarshe na Kotun Ƙoli."

Sanatan ya kuma yi fatan al'umma za su cigaba da Addu'a ta Alkhairi da kuma ɗorewar zaman lafiya a jihar Kano da kuma Najeriya baki ɗaya.

Rikicin APC a Kano

Jam'iyya mai mulki ta shiga halin rikici ne a jihar Kano bayan bayyanar shugabannin APC reshen Kano guda biyu, tsagin gwamna Ganduje da kuma Sanata Shekarau.

Kara karanta wannan

Naziru Sarkin Waka ya tubewa 'Yan wasan fim zani a kasuwa yayin da ya kare Almajirai

Kowane tsagin daga cikin ɓangarorin biyu ya yi iƙirarin cewa shi ne halastacce da uwar jam'iyya ta sani, hakan ya ja lamarin har gaban Kotu.

A halin yanzu, Batun na gaban Kotun Ƙoli bayan kotun ɗaukaka ƙara da tabbatar da ingancin tsagin Ganduje.

A wani labarin kuma Fitattun Attajirai biyu sun lale miliyan N200m zasu siyawa mutum biyu Fom ɗin takarar shugaban ƙasa a APC

Wasu yan kasuwa guda biyu yan asalin jihar Abia sun shirya lale makudan kuɗi Miliyan N200m don siya wa mutum biyu Fom a APC.

A wata sanarwa da suka fitar a Abuja, fitattun Attajiran sun ce sun gano kwarewa da salon mulki a jikin Sanata Ahmad Lawan da Orji Kalu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel