Kaduna: Fuskokin Mutanen Da Aka Kama Kan Satar Tankar Mai Ɗauke Da Fetur Na N6.2m

Kaduna: Fuskokin Mutanen Da Aka Kama Kan Satar Tankar Mai Ɗauke Da Fetur Na N6.2m

  • Yan sanda a Jihar Kano sun yi nasarar kama wasu mutane shida da ake zargi da satar man fetur a Kaduna
  • Bata garin sun tare wata tanka ne dauke da fetur lita 40,000 da kudinsu ya kai N6.2m suka gudu da shi
  • Daga bisani an gano gidan man da suke zuwa su sayar da fetur din satan an kuma kama masu gidan man da sauran wadanda ake zargi

Jihar Kaduna - Rundunar yan sandan Jihar Kaduna ta kama mutane shida da ake zargi da satar tanka makare da man fetur lita 40,000 da kudinsa ya kai Naira miliyan 6.2 a jihar, rahoton The Guardian.

The Punch ta rahoto cewa bayanin na kunshe cikin sanarwar da kakakin rundunar, Mohammad Jalige, ya fitar ne a ranar Litinin.

Kara karanta wannan

Karfin hali: Dan Najeriya ya fusata, ya maka Buhari a kotu saboda gallazawa 'yan Najeriya

Kaduna: 'Yan Sanda Sun Kama Mutum 6 Kan Satar Tankar Mai Ɗauke Da Fetur Na N6.2m
'Yan Sanda a Kaduna Sun Kama Mutum 6 Kan Satar Tankar Ɗauke Da Fetur Na N6.2m. Hoto: Guardian Nigeria.
Asali: Twitter

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A cewar Jalige, a ranar 19 ga watan Afrilun 2022, rundunar ta samu korafi daga wani Bukura Bukar na Maraban Jos, Kaduna cewa a ranar 16 ga watan Afrilun 2022, ya damka motar mai lamba BAM 02 XA, dauke da man fetur lita 40,000 da kudinsa ya kai N6.2m hannun direbansa daga Legas zuwa Kaduna.

Ya ce bayan motar ta lalace saboda taya, wasu mutane uku a mota kirar Sedan suka kai wa direban hari da yaron mota, suka tsere da man fetur din.

Yadda aka kama wadanda ake zargin

Da taimakon bayanai da aka samu, Jalige ya ce jami'an rundunar sun bazama sun gano gidan man da aka kai fetur din tare da kama wasu cikin wadanda ake zargin.

Wani sashi na sanarwar ta ce:

Kara karanta wannan

Karin bayani: Yan bindiga sun sace wata mai taimakon talakawa da diyarta a Kaduna, sun nemi a biya N100m

"Yan sanda bisa bayannan sirri sun yi nasarar kama wasu mutum uku da ake zargi; Habibu Mohamed, Halilu Mohammed da Isa Mohammed.
"Binciken da aka cigaba da yi ya nuna cewa akwai gidajen mai biyu da ake kai kayan satar. An kama masu gidan man da ake zargin abokan harkallar wadanda ake zargin ne. Sun hada da Isa Yusuf, Surajo Lawal da Stephen Habila.
"An kuma gano motar da bata garin ke amfani da ita, wuka guda daya da tankar man da aka sace da fetur din."

Ya ce wadanda ake zargin sun amsa laifinsu kuma ana cigaba da zurfafa bincike kan lamarin.

Kwastam Ta Kama Motar Dangote Makare Da Buhun Haramtaciyyar Shinkafar Waje 250

A wani rahoton, Kwantrolla Janar na Kwastam, Team A Unit, Mohammed Yusuf, ya ce jami'an hukumar sun kwace wata motar babban Dangote makare da buhun shinkafa na kasar waje 250 da aka haramta shigo da su.

Kara karanta wannan

Da dumi-dumi: NDLEA ta kai samame wurin bikin casu a Abuja, ta cafke jama'a da yawa

Yusuf ya bayyana hakan ne a ranar Alhamis a Ikeja, Legas, yayin taron manema labarai inda ya bada jawabin ayyukan da suka yi cikin makonni hudu a sassa daban-daban, The Punch ta ruwaito.

Ya bayyana cewa a cikin kayan da aka kwace akwai kwantena ta katako mai tsawon kafa 20; buhunan shinkafa masu nauyin 50kg guda 1000; taya na gwanjo guda 3,143; kunshin tufafin gwanjo 320; Buhun fatar jaki 44 da ganyen wiwi kilogiram 137.3.

Asali: Legit.ng

Online view pixel