'Yan ta'addan ISWAP sun yi ikirarin alhakin halaka 'yan sanda 3 a Kogi

'Yan ta'addan ISWAP sun yi ikirarin alhakin halaka 'yan sanda 3 a Kogi

  • Mayakan ISWAP sun tabbatar da yadda suke da alhakin kai hari wani ofishin 'yan sanda a jihar Kogi a wata takarda da kungiyar ta saki a Telegram
  • An ruwaito yadda 'yan bindiga suka kai farmaki wani ofishin'yan sanda a karamar hukumar Adavi a safiyar Asabar, gami da halaka 'yan sanda uku
  • Yayin da kwamishinan'yan sandan jihar ya siffanta lamarin a "harin ba-zata", kwamandan ISWAP ya kara da cewa sune keda alhakin saka abu mai fashewa a wata kasuwa a jihar Taraba

Kogi - Kungiyar ta'addanci ta ISWAP ta tabbatar da alhakin kaiwa wani ofishin 'yan sanda hari a jihar Kogi.

The Cable ta ruwaito yadda 'yan bindiga suka kai hari wani ofishin 'yan sanda a karamar hukumar Adavi a safiyar Asabar, gami da halaka 'yan sanda uku.

Kara karanta wannan

Da duminsa: An damke wani mai hadawa yan ta'addan IPOB Bam a Kudu maso gabas

'Yan ta'addan ISWAP sun yi ikirarin alhakin halaka 'yan sanda 3 a Kogi
'Yan ta'addan ISWAP sun yi ikirarin alhakin halaka 'yan sanda 3 a Kogi. Hoto daga thecable.ng
Asali: UGC

Edward Egbuka, kwamishinan 'yan sandan jihar, ya siffanta mummunan lamarin a matsayin "harin ba-zata."

Kamar yadda Voice of America ta bayyana, a wata takarda da ISWAP ta wallafa a Telegram, ta ce "Sojojin Halifan Musulunci sun kai wa ofishin 'yan sanda hari."

Kungiyar ta kara da bayyana yadda aka halaka mutane biyar yayin kai harin.

Haka zalika, ISWAP ta bayyana yadda take da alhakin saka abu mai fashewa, wanda ya lashe rayukan mutane shida a kasuwa cikin Taraba a ranar Talata.

Inda kuwa kungiyar 'yan ta'addan ne ke da alhakin kai hare-haren da tayi ikirari, hakan na nuna yadda kungiyar ta'addancin ke kara kamari a yankin arewancin kasar.

Duk da dai Taraba jiha ce a arewa maso gabas, inda ISWAP da Boko Haram ke cin karensu ba babbaka, ba a cika kaiwa jihar hari ba, kamar yadda ake kai hari Borno da Yobe. Harin da aka kai cikin kwanakin nan ya jefa mazauna yankin cikin matsananciyar damuwa.

Kara karanta wannan

Katsina: 'Yan sanda sun halaka 'yan ta'adda 2, sun ceto wasu da aka yi garkuwa da su

Bugu da kari, harin da kungiyar ta kai ofishin 'yan sanda, wanda ba a taba samun haka ba a baya, alama ne dake nuna cewa ISWAP na ko ina a yankin arewa.

Rahotanni masu karo da juna kan bidiyon sojoji sun kwashe 'yan ta'adda a motocinsu a Kaduna

A wani labari na daban, rudani ya bibiyi wani bidiyo da ke ta yawo wanda ke bayyana sojin Najeriya sanye da khaki suna kwashe wasu mutane da ake zargin 'yan bindiga ne zuwa motar sojoji.

Mutane da yawa sun zargi cewa 'yan bindiga ne da suka kutsa yankin Kakura da ke karamar hukumar Chikun ta jihar Kaduna a ranar Lahadi.

Wani mazaunin Kakura ya sanar da Daily Trust cewa sojoji da 'yan sa kai sun halaka 'yan bindiga 16 a lokacin da suka kutsa yankin wurin karfe 11 na daren Asabar. Ya ce wasu 17 sun jigata bayan artabun da suka yi da jami'an tsaro.

Kara karanta wannan

Da dumi: Yan Boko Haram sun kai hari mashaya a Yobe, sun kashe 9, sun kona Kwalejin Fasaha

Asali: Legit.ng

Online view pixel